Shekarau ya danganta komawar sa APC daga PDP da hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina

Shekarau ya danganta komawar sa APC daga PDP da hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina

- Shekarau ya danganta komawar sa APC daga PDP da hijirar manzon Allah

- Yace ya dawo APC ne saboda ya yaki rashin adalcin da aka yi masa

- Wasu sun soki tsohon gwamnan a kan kalamin na sa

A yau ne dai tsohon gwamnan Kano, Alhaji Ibrahim Shekarau ya sanar da ficewar sa daga jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party, (PDP) zuwa jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC) a garin Kano.

Shekarau ya danganta komawar sa APC daga PDP da hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina
Shekarau ya danganta komawar sa APC daga PDP da hijirar manzon Allah daga Makka zuwa Madina
Asali: Twitter

KU KARANTA: Atiku ya sha ihun 'ba mayi, sai Buhari' a masallacin juma'a a Kaduna

Sai dai wani batu da ya dauki hankalin al'umma musamman ma mabiya addinin musulunci a jihar da ma kasar baki daya shine na yadda aka ruwaito tsohon gwamnan ya kwatanta sauyin shekar ta sa da hijirar Manzon Allah, Annabi Muhammadu SAW, daga Makka zuwa madina.

Legit.ng ta samu cewa majiyar mu ta tsinkayi tsohon gwamnan a lokacin da yake yiwa dumbin magoya bayan sa jawabin dalilin komawar ta sa yana cewa:

"Annabi (SAW) Ma Da Aka Matsa Masa Hijira Ya Yi Daga Makka Zuwa Madina, Daga Bisani Kuma Ya Dawo Ya Yaki Makka Har Ya Samu Nasara. Don Hakan Ni Ma Na Yi Hijira Daga PDP Ne Zuwa APC Domin Yakar Zalunci Da Son Zuciya, Don Haka Daga Yau Ni Da Masoyana Mun Yi Kuara Daga PDP Zuwa APC".

Sai dai wasu jama'a musamman ma 'yan jam'iyyar ta PDP da dama na ganin wannan kalamin sam bai kamata ya fito daga bakin sa ba yayin da kuma magoya bayan tsohon gwamnan suke ganin misali ne kawai ya bayar don haka ba komai.

Ga dai faifan bidiyon nan:

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel