Diyar manya, matar manya: Ku sadu da Halima Dangote, babbar diyar hamhsakin mai kudi Aliko Dangote

Diyar manya, matar manya: Ku sadu da Halima Dangote, babbar diyar hamhsakin mai kudi Aliko Dangote

- Mutane da dama sukan yi tunanin ko suwaye 'ya'yan fitattun masu kudin duniya?

- Kuma ko yaya suke rayuwa?

- A ina suke zama kuma su waye abokanan su?

Wadannan dai dama wasu sauran tambayoyin ka iya bijiro wa zuciyar mutum idan yaji ance ga 'yayan fitaccen mai kudin nan dan kasuwa dan asalin jihar Kano wato, Alhaji Aliko Dangote.

To dai shi nashi 'ya'yan, abun da zai ba mai karatu mamaki shine yadda su kwata-kwata ma basu dauki duniya da zafi ba don kuwa suna rayuwar su ne tamkar yadda saura keyi ba tare da wani banbanci ba.

Diyar manya, matar manya: Ku sadu da Halima Dangote, babbar diyar hamhsakin mai kudi Aliko Dangote
Diyar manya, matar manya: Ku sadu da Halima Dangote, babbar diyar hamhsakin mai kudi Aliko Dangote
Asali: Facebook

KU KARANTA: Sarkin musulmi ya soki gwamnatin Buhari a kaikaice

Shi dai fitaccen mai kudin nan dan kasuwa dan asalin jihar Kano wato, Alhaji Aliko Dangote Allah ya albarkace shi da 'ya'ya uku kacal kuma duk mata a duniya a aure biyu da yayi a rayuwar sa. Duk da dai kusan a iya cewa 'ya'yan sa hudu domin akwai wani namiji da yake riko.

Legit.ng ta samu cewa 'ya'yan na fitaccen maikudin sun hada da Halima Dangote, Mariya da kuma Fatima. Ita Halimar itace babba, kuma akan ta za mu dan takaitaccen rubutun mu na yau.

Ita dai Halima ta yi karatun ta na digiri ne a makarantar koyon kasuwanci a jami'ar American Intercontinental, birnin Landan.

Haka zalika tayi karatun ta na digiri na biyu a birnin Landan din duk dai akan ilimin kasuwancin domin ta gaji baban ta.

Hanzu haka kuma tayi auren ta agarin Kano da wani hamshakin mai kudin shima mai suna Sulaiman Sani Bello kuma suna da 'ya'ya biyu kyawawa.

Haka zalika mun samu cewa tana kula da kasuwancin babanta sosai.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel