Tsintsiya ta watse: Sabuwar cakwakiya ta bulla a jam'iyyar APC ta jihar Sokoto

Tsintsiya ta watse: Sabuwar cakwakiya ta bulla a jam'iyyar APC ta jihar Sokoto

- Sabuwar cakwakiya ta bulla a jam'iyyar APC ta jihar Sokoto

- Yan kungiyar APC Adalci Buhari Sak sunce sam basu amince da tsarin jam'iyyar ba wajen fitar da 'yan takara

- Sunce su suna tare da Shugaba Buhari da manufofin sa

Wata sabuwar rigima da ka iya kawo babbar baraza ga jam'iyyar adawa ta All Progressives Congress (APC), a jihar Sokto ta bulla inda wasu daga cikin jiga-jigan jam'iyyar suka kekashe kasa sukayi fatali da tsarin zaben fitar da gwani na deliget da jam'iyyar tace za ta yi.

Tsintsiya ta watse: Sabuwar cakwakiya ta bulla a jam'iyyar APC ta jihar Sokoto
Tsintsiya ta watse: Sabuwar cakwakiya ta bulla a jam'iyyar APC ta jihar Sokoto
Asali: Twitter

KU KARANTA: Sarkin musulmi ya soki Shugaba Buhari a kaikaice

Ya'yan jam'iyyar dai ta APC da suka kira kansu da suna APC Adalci Buhari Sak, sunce sam basu amince da bin wannan tsarin ba a jihar domin kuwa akwai munakisa da shigar hanci da kudundune da tsarin ke cike da shi.

Legit.ng ta samu cewa shugaban yan jam'iyyar dake kiran kan su APC Adalci Buhari Sak Farfesa Muhammad Lawal Bashar shine ya sanar da matsayar ta su jim kadan bayan sun kammala wani taron su.

Farfesa Muhammad yace su suna tare da matsayar uwar jam'iyya game da tsarin gudanar za zabukar fitar da gwani na kato bayan kato kuma ba za su amince da dukkan wata kwaskwarima da za a fito masu da shi ba.

Haka zalika ya kara da jaddada goyon bayan su ga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da yin alkawarin za su cigaba da yi masa biyayya sau da kafa a dukkan harkokin kungiyar a cikin jam'iyyar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel