Yan majalisa 12 a jihar Sokoto sun yiwa Gwamna Tambuwal taron dangi

Yan majalisa 12 a jihar Sokoto sun yiwa Gwamna Tambuwal taron dangi

- Yan majalisa 12 a jihar Sokoto sun yiwa Gwamna Tambuwal taron dangi

- Yan majalisar sun siya ma Faruok Malami Yabo fom din takarar Gwamna

- Faruok Malami Yabo yana da farin jini sosai

Akalla 'yan majalisar dokoki a jihar Sokoto su goma sha biyu ne da a baya suka ki bin gwamnan jihar su Aminu Waziri Tambuwal lokacin da ya koma People’s Democratic Party (PDP) ne suka tara kudi suka kuma siyo fom din takarar Gwamna ga Faruok Malami Yabo.

Yan majalisa 12 a jihar Sokoto sun yiwa Gwamna Tambuwal taron dangi
Yan majalisa 12 a jihar Sokoto sun yiwa Gwamna Tambuwal taron dangi
Asali: Facebook

KU KARANTA: An kama gawurtattun matsafa 13 a Najeriya

Shugaban gamayyar 'yan majalisar ne dai Honarabul Sani Alhaji Yakubu ya bayyanawa manema labarai hakan a jihar inda yace yanzu duk hankalin su ya raja'a ne wajen ganin an samu canjin gwamnati a jihar a zaben 2019 mai zuwa.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Honarabul Sani Alhaji Yakubu yace sam ba za su taba yin kasa a gwuiwa ba har sai sun tabbata sun karbo mulki daga hannun 'yan PDP a jihar sun kuma damka shi a hannun APC wadda dama na su ne.

Mun samu dai cewa Alhaji Faruk Malami Yabo, fitaccen dan siyasa ne kuma hamshakin mai kudi gami da dumbin magoya baya a jihar kuma ya taba yin kwamishinan harkokin kudi da kananan hukumomi a jihar.

A wani labarin kuma, kwamiti na musamman da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada domin kwato dukkan dukiyar al'ummar da wasu ma'aikatan gwamnati suka yi sama da fadi da su a cikin garin Abuja ya samu nasarar kwato motoci 19.

Motocin dai kamar yadda muka samu, kwamitin ya kwato su ne daga hannun tsaffin ma'aikatan hukumar nan ta kidayar al'umma ta kasa watau National Population Commission (NPopC) a turance.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel