Yanzu yanzu: Wata kungiya a Daura ta tara N70m don yakin zaben Buhari da Masari

Yanzu yanzu: Wata kungiya a Daura ta tara N70m don yakin zaben Buhari da Masari

- Wata kungiya a Daura, jihar Katsina, ta tara N70m don gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Kungiyar ta kuma ce zata yi amfani da kudaden wajen gudanar da yakin neman zaben gwamnan jihar, Aminu Bello Masari

- A cewar kungiyar, an tara kudin ne daga karo karo da mambobin kungiyar suka yi da nufin daukar nauyin yakin zaben shuwagabannin biyu

Wata kungiya mai zaman kanta a jihar Katsina, mai fafutukar bunkasa rayuwar matasan yankin Daura (DEYPM), ta ce ta tara Naira Miliyan 70 don gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma gwamnan jihar Aminu Bello Masari a zaben 2019 da ke gabatowa.

Abdulkadir Lawa, shugaban shiyya na kungiyar, ya bayyana hakan a wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Asabar, 8 ga watan Satumba, a garin Daura.

Lawal ya ce daga cikin kudin, za'a batar da N40m ga shugaban kasar, yayin da za'a batar da N30m ga gwamnan jihar, Aminu Bello Masari, don gudanar da yakin neman zabensu, da nufin tazarce a 2019.

KARANTA WANNAN: Siyasar Kano ta dau zafi: APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019

Yanzu yanzu: Wata kungiya a Daura ta tara N70m don yakin zaben Buhari da Masari
Yanzu yanzu: Wata kungiya a Daura ta tara N70m don yakin zaben Buhari da Masari
Asali: Depositphotos

Lawal wanda ya ce an samar da kudin ne daga karo karo daga jama'ar gari, kungiyoyi da kuma mambobin kungiyar da nufin daukar nauyin gudanar da yakin neman zaben shuwagabannin biyu, ya ce za'ayi amfani da kudin wajen daukar hayar motoci, da sauran kayayyakin gudanar da yakin enman zaben a kananan hukumomi 5 na shiyyar Daura.

Ya ce sun yanke wannann hukunci ne duba da irin ayyukan raya kasa da shuwagabannin biyu suka kawo a shiyyar, da suka hada da kawo jami'ar sufuri ta gwamnatin tarayya da kuma wani sansanin horas da sojoji da dai sauransu.

Shugaban kungiyar na shiyya, wanda ya kuma ce da farko sun yi niyyar siyawa Buhari fom din tsayawa takara amma wasu suka riga su, ya jinjinawa kungiyar da ta biya kudin fom din tare da yin fatan samun nasarar zaben 2019.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel