An bani kudi don janye karar da na shigar akan wanda ya kashe min yarona amma naki karba - Wani mahaifi

An bani kudi don janye karar da na shigar akan wanda ya kashe min yarona amma naki karba - Wani mahaifi

- Rundunar yan sanda ta kori Gbadamosi Lukman, jami'in SARS, wanda ake zargi da kashe Nafiu Tunde a jihar Osun.

- Mahaifin yaron da aka kashe, Chief Saditu Nafiu Ayodele, ya yi ikirarin cewa an yi masa tayin kudi don janye karar amma ya ki amincewa.

- An yi zargin cewa Gbadamosi ya harfe Nafiu a kan hanyar sa daga Ile-Ogbo, wani gari da ke cikin karamar hukumar Ayedere, a ranar Alhamis, 23 ga watan Augusta, 2018.

Rundunar yan sanda ta kori Gbadamosi Lukman, jami'in runduna ta musamman da ke dakile fashi da makami da garkuwa da mutane, wanda ake zargi da kashe Nafiu Tunde a jihar Osun.

Mahaifin yaron da aka kashe, Chief Saditu Nafiu Ayodele, ya shaidawa SaharaReporters cewa, "An kai Lukman kotun majistire dake Osogbo a ranar Alhamis, daga nan ne aka yanke hukuncin korarsa daga aiki, tare da ajiye shi a gidan kurkuku na Ilesha"

"Kotun ta ce zata mika shari'ar ga Antoni Janar na kasa kuma kwamishinan shari'a, Dr. Surajudeen Ajibola Basiru"

Ya kuma yi ikirarin cewa an yi masa tayin kudi don janye karar amma ya ki amincewa.

KARANTA WANNAN: Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin fushi idan ka yaudare shi - Lawal

Hoton Tunde Nafiu, a lokacin da ya ke raye
Hoton Tunde Nafiu, a lokacin da ya ke raye
Asali: Facebook

Ya ce: "An yi min tayin kudi don janye karar daga kotu amma ban karba ba. Tun a lokacin suke tuntubar na kusa da ni don bani hakuri, don karbar kudin tare da janye karar ba tare da kowa ya ji ba.

"Sirikin Lukman basarake ne a yankin Ife, jihar Osun. Ya zo har inda nike tare da yan majalisun fadarsa, sun roke ni amma naki amincewa"

An yi zargin cewa Gbadamosi ya harfe Nafiu a kan hanyar sa daga Ile-Ogbo, wani gari da ke cikin karamar hukumar Ayedere, a ranar Alhamis, 23 ga watan Augusta, 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel