Ya gamu da ajalisa yana kokowa da kwarton da ya kama turmi da tabarya da matarsa a kan gadon aurensu

Ya gamu da ajalisa yana kokowa da kwarton da ya kama turmi da tabarya da matarsa a kan gadon aurensu

- Dole rikici ya barke bayan da wani mutumi ya kama matarsa da wani kwarto suna fasikanci akan gadon aurensu

- Ba tare da bata lokaci ba mijin ya cewa kwarton da wa Allah ya hadani inba da kai ba, suka kaure da kokowa

- Sai dai kamar karin maganar malam Bahaushe, idan ajali ya yi kira, ko babu ciwo za'a je. A wannan kokowarne mijin ya gamu da ajalinsa

Rahotannin da muka samu yanzu na nuni da cewa wani magidanci dan kasar Kenya, da aka bayyana sunan sa da Dikson Samba, ya kama matarsa da wani kwarto suna fasikanci a kan gadon aurensu, bayan da ya dawo gidan ba tare da ya sanar da matar dawowarsa ba.

Sai dai mutumin ya gamu da ajalinsa a lokacin da yake kokowa da kwarton, a gidansa da ke jerin rukunin gidajen Umoja, Nairobi.

Kamar dai yadda kowane magidanci zai dau hukunci a irin wannan yanayi, musamman ma idan ya zamana cewa yana da masifar kishi, bayan da Dickson ya dawo gida ya taras da matarsa da kwarto a halin turmi da tabarya, nan take kuwa ya jawo mutumin, inda suka fara kokowa a tsakiyar dakin.

Ya gamu da ajalisa yana kokowa da kwarton da ya kama turmi da tabarya da matarsa a kan gadon aurensu
Ya gamu da ajalisa yana kokowa da kwarton da ya kama turmi da tabarya da matarsa a kan gadon aurensu
Asali: Depositphotos

Sai dai cikin tsautsayi, Dickson ya zame ya fado kasa daga hawa na hudu na ginin da suke ciki, a sanadiyyar faduwarsa, kansa ya bugi wani damali da yake a waje, nan take ya ce 'ga garinku nan', sakamakon mummunan raunin da ya ji a kansa.

A cewar wasu da lamarin ya afku a gaban idanunsu, sun ce kwarton matar ne ya fi karfinsa,inda ya jefo shi daga saman dakinsu da ke a hawa na hudu, inda ya fado a saman kansa, sakamakon haka ya mutu nan take.

Sai dai, kwarton matar ya samu nasarar tserewa daga wajen kafin a kama shi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel