Tura ta kai bango: APC jam'iyyar batattu ce - Makarfi

Tura ta kai bango: APC jam'iyyar batattu ce - Makarfi

- Sanata Ahmed Makarfi, ya ce a yanzu batattu ne ke jagorantar Nigeria, kwatankwacin wadanda suke tafiya a kwale kwale, ya jirkice suka nutse a ciki

- Makarfi ya kara jaddada bukatar sake fasalin kasar, idan har ana son samar da ingantaccen ci gaba

- Ministan watsa labarai, Sanata Patricia Akwashiki, ta ce ita ce zata fara zama mace ta farko a Nigeria da zata zama Gwamna, wato kallabi tsakanin rawuna

A ranar Juma'a, 7 ga watan Satumba, tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi, ya ce a yanzu batattu ne ke jagorantar Nigeria, kwatankwacin wadanda suke tafiya a kwale kwale, ya jirkice suka nutse a ciki.

Makarfi wanda ya isa sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja don maida fom din nuna sha'awa da kuma tsayawa takarar shugaban kasa a zaben fitar da gwani na jam'iyyar, ya kuma ce shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kasa cika alkawarin da ya dauka na biyan marasa karfi N5,000 ko wane wata.

Da ya ke jajantawa magoya bayan jam'iyyar bisa harin da wasu yan ta'adda, da ake zargin jam'iyyar APC ce ta turo su, suka kai sakatariyar a ranar Alhamis, Makarfi ya ce, "Irin wannan bai taba faruwa ba, wai ace jam'iyya ta ketare iyakarta ta shiga gonar wata jam'iyyar don neman fada, amma babu mugun tuggun da zasuyi, su samu nasara.

KARANTA WANNAN: Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

Gugar zana: APC jam'iyyar batattu ce - Makarfi
Gugar zana: APC jam'iyyar batattu ce - Makarfi
Asali: Depositphotos

"Cin mutunci ba zai yi aiki a nan ba, muna sane da cewa mambobin APC sun tsorata da PDP, don haka ba zamu taba maida hankalinmu akan su ba har mu sake su samu galaba a kanmu, zasu iya amfani da duk abinda suka ga dama, mu kuma zamuyi amfani da kwakwalwarmu wajen finsu tunani"

Makarfi ya kara jaddada bukatar sake fasalin kasar, idan har ana son samar da ingantaccen ci gaba.

Ya ce, "Wannan kudiri ne na jam'iyyar PDP, na sake fasalin kasar don ci gaban yan kasar baki daya. Ya zama wajibi mu ceto Nigeria daga mawuyacin halin da take ciki yanzu, dole ne mu dawo da hadin kai da kuma dakatar da wannan zubar da jinin da ake yiwa wadanda basu ji ba basu gani ba"

A wani labarin kuma, Ministan watsa labarai, Sanata Patricia Akwashiki, ta ce ita ce zata fara zama mace ta farko a Nigeria da zata zama Gwamna, wato kallabi tsakanin rawuna.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel