Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin fushi idan ka yaudare shi - Lawal

Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin fushi idan ka yaudare shi - Lawal

- Babban dalilin da ke harzuka Adam A Zango, kuma ya sanya shi yin fushi a nan take, shine ya gano ka yaudare shi, irin yaudarar nan ta rainin wayau

- Wasu lokutan ya zabi ya zauna tare da abokansa, ko kananan yara, suna wasa da dariya, Adam A Zango mutum ne mai saukin kai, idan har ka fahimce shi

- A ranar 6 ga wannan watan da muke ciki, Adam A Zango, ya roki gafarar Ali Nuhu, don kawo karshen takun sakar dake tsananinsu

A cikin labaran da muke kawo maku daga dandalin Kannywood, a yau Legit.ng ta duba wani bangare na rayuwar jarumi a masana'antar shiry fina finan Hausa, wanda ya fara wannan sana'a da kida, waka, daga bisani likafarsa ta ci gaba, har zuwa yau da wasu ke masa lakabi da 'Yariman Kannywood'.

Kamar yadda kowane dan Adam ya ke da fuska biyu; fushi da dariya, haka shima jarumi Adam A Zango ya ke. Akwai abubuwa da dama da suke sanya shi farin ciki, wasu kuma su sanya shi bakin ciki. Sai dai, dole ne a samu muhimmai daga cikinsu, wadanda mutum ke harzuka matuka akansu, ko kuma ya tsinci kansa cikin matsanancin farin ciki akansu.

A bangaren Adam a Zango, ko wadanne muhimman abubuwa ne ke sanya shi saurin fushi?

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta zanda da wani dan uwan Adam A Zango, dan kasuwa kuma dan siyasa, Lawal Idiya Usman, ya bayyana manyan dalilan da ke saurin harzuka jarumin, da kuma wadanda ke sanya shi farin ciki, kasancewar sunyi kuruciyarsu a tare.

KARANTA WANNAN: Siyasar Kano ta dau zafi: APC ta yiwa Shekarau alkawarin kujerar Kwankwaso a zaben 2019

Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin Fushi idan ka yaudare shi - Lawal
Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin Fushi idan ka yaudare shi - Lawal
Asali: Facebook

"Adam A Zango mutum ne mai saukin kai, wanda ya ke da saukin mu'amala. Baya son shiga rigingimu, sau tari yakan kauracewa wuraren da ake yawan gardama, koda kuwa da shi ake yi, ko da kuwa shi ne ya ke da gaskiya, ya zabi ya bar wajen da ayi gardama da shi, saboda yana da saurin fushi" a cewar Lawal Idiya Usman.

Ko da aka tambaye shi abubuwan da ke harzuka Adam A Zango nan take, Lawal Idiya ya ce: "Babban abinda ke harzuka shi, ya sanya shi fushi a nan take, shine ya gano cewaka yaudare shi, irin yaudarar nan ta rainin hankali. Idan har ya gano kana yi masa dan-waken zagaye, to tabbas mai rabaku sai Allah"

Idan ba'a manta ba, a karshen watan Disamba, 2017, Legit.ng, ta ruwaito maku yadda Adam A Zango ya bayyana fushinsa kan yadda mutane ke cinsa gyara a duk lokacin da yayi magana da turanci.

Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin Fushi idan ka yaudare shi - Lawal
Dandalin Kanywood: Adam A Zango na da saurin Fushi idan ka yaudare shi - Lawal
Asali: Facebook

KARANTA WANNAN: Bincike ake yi: Kwamitin shugaban kasa ya kawoto motoci 19 daga tsofaffin jami'an gwamnati

A lokaci n Zango ya ce: "Yau zanyi wata magana, wacce na san ba zatayiwa masoyana dadi ba, dangane da gyaran da wasu ke ci na idan nayi turanci. Shin dama na taba fadi maku cewa na je makaranta? Ni ban taba zuwa makaranta ba, akwai na koyi turancin ne a kan titi, don haka koda ace ba dai-dai na ke yi ba, bai kamata ya zama abun wulakantani da shi ba"

Ko me ke sanya Adam A Zango farin ciki?

Da aka tambayi Lawal Idiya Usman, abubuwan da ke sanya jarumin farin ciki,ya ce: "Abubuwan ban dariya, ka kasance kana yi masa maganganun raha. Wasan barkwanci na matukar burge shi. Wasu lokutan ya zabi ya zauna tare da abokansa, ko kananan yara, suna wasa da dariya. Adam A Zango mutum ne mai saukin kai, idan har ka fahimce shi"

A wani labarin makamancin wannan:

A ranar 6 ga wannan watan da muke ciki, Adam A Zango, ya kawo karshen gabar da ke tsakaninsa da babban jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, wanda akewa lakabi da 'Sarkin Kannywod', Ali Nuhu, bayan da Zango ya roki gafarar Ali Nuhu.

Adam A Zango ya roki afuwar Ali Nuhu
Adam A Zango ya roki afuwar Ali Nuhu
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar PremiumTimes ta ruwaito, jarumin ya roki wannan gafarar ne a shafinsa na Instagram, inda ya dora hotonsa, yana durkushe saman guiwowinsa a gaban Ali Nuhu, inda ya rubuta "Sarki Ali, ina durkushe a saman guiwowina, ka gafarta min alifukan da nayi maka".

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel