Gawurtattun matsafa 13 sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya

Gawurtattun matsafa 13 sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya

- Jami'an 'yan sandan Najeriya sun cafke wasu 'yan kungiyar asiri 13

- Gawurtattun matsafa 13 sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya

- Matsafan sun addabi al'ummar jihar da makwafta

Jami'an 'yan sandan Najeriya, shiyyar jihar Kwara sun sanar da samun nasarar cafke wasu gawuratattun matsafa 'yan kungiyar asirin nan ta Badoo da suka addabi al'ummar jihar.

Gawurtattun matsafa 13 sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya
Gawurtattun matsafa 13 sun shiga hannun jami'an tsaron Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun harbe wani malamin addini a Najeriya

Majiyar mu ta Tribune, ta tabbatar mana da cewa jami'an 'yan sandan sun cafke matsafan ne bayan wani samame da suka kai masu sakamakon bayanan sirri da suka samu daga wasu masu kishin kasa.

Legit.ng ta samu cewa jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar Ajayi Okasanmi ya bayyana cewa suna nan suna bincike a kan su kuma da sun kammala za su kai su kotu domin a yanke masu hukunci.

Mai karatu dai idan bai manta ba 'yan kungiyar asirin a watannin baya sun addabi al'ummar jihar da ma makwafta inda sukan kashe jama'a su kuma yi tsafi da wasu sassa na jikin su.

A wani labarin kuma, Wani matashin saurayi mai suna Prince dake a makarantar Sakandare ta jeka-ka-dawo ta Isaac Jasper Boro a karamar hukumar Sagbama, jihar Bayelsa ya kashe kansa lokacin da ya gano wani saurayi ya kwace masa budurwa.

Shi dai Prince wanda akace dan asalin kauyen Kaiama ne a karamar hukumar Kolokuma/Opokuma ance ya kwankwadi maganin kwari na fiya-fiya ne wanda sandiyyar haka ya margaya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel