Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda 3 da yan banga 2 a Taraba

Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda 3 da yan banga 2 a Taraba

- Yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kashe jami’an yan sanda uku da yan banga biyu a jihar Taraba

- Lamarin ya faru ne a yau Juma'a 7 ga watan Satumbaa

- Sun kuma tafi da makamai mallakar yan sandan

Wasu yan bindiga da ba’a san ko su wanene ba sun kashe jami’an yan sanda uku da yan banga biyu a Bujum Kasuwan dake karamar hukumar Lau na jihar Taraba a ranar Juma’a, 7 ga watan Satumba.

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa yan sandan da yan bangan na aikin bincike ne a yankin lokacin da yan bindigan suka far masu sannan suka kashe su.

Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda 3 da yan banga 2 a Taraba
Yan bindiga sun kashe jami’an yan sanda 3 da yan banga 2 a Taraba
Asali: Depositphotos

An tattaro cewa tawagar na karkashin jagorancin wani jami’in kula da masu laifi mai suna ASP Kilobas Iliya zuwa yankin wadda suka fuskanci rikicin kabilanci a kwanan baya.

KU KARANTA KUMA: Jihohi 12 zasu fuskanci ambaliyar ruwa – NEMA da NHISA sunyi gargadi

Yan bindigan sun tafi da bindigar AK47 da wani karamin bindiga mallakin yan sandan bayan sun kashe su.

Kakakin yan sandan jihar Taraba, ASP David Misal ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Yace kwamishinan yan sandan jihar, David Akinremi yayi umurni ga ayi bincike akan lamarin cikin gaggawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel