Masana sun bada labarin musabbabin aukuwar girgizar kasa a Abuja

Masana sun bada labarin musabbabin aukuwar girgizar kasa a Abuja

- Masana sun bada labarin musabbabin aukuwar girgizar kasa a Abuja

- Sunce hakan na iya kasantuwa ta dalilin fasa duwatsu barkatai da al'umma ke yi

- Sunce ya kamata ayi doka kan hakan

Masana a fannin ilimin kimiyya da fasaha sun bayyana cewa 'yar girgizar kasar da aka samu a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya a yau din nan na iya kasantuwa ta dalilin fasa duwatsu barkatai da al'umma ke yi.

Masana sun bada labarin musabbabin aukuwar girgizar kasa a Abuja
Masana sun bada labarin musabbabin aukuwar girgizar kasa a Abuja
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kanin wani dan takarar shugaban kasa a PDP zai koma APC

A don haka ne ma masanan sukayi kira ga mahukunta da su waiwayi batun su kuma yi kokarin samar da dokar da zata hana ayyukan fashe-fashen duwatsun ba bisa ka'ida ba domin kaucewa sake aukuwar lamarin.

Legit.ng ta samu cewa wannan tsokacin dai ya fito ne daga bakin Farfesa Motso Onuoha dake zaman shugaban gamammiyar kungiyar malaman masana ilimin kimiyya da fasaha ta kasa.

Mai karatu dai idan bai manta ba a dazu ne muka kawo maku labarin aukuwar 'yar karamar girgizar kasa a garin na Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

A wani labarin kuma, Kwamiti na musamman da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya nada domin kwato dukkan dukiyar al'ummar da wasu ma'aikatan gwamnati suka yi sama da fadi da su a cikin garin Abuja ya samu nasarar kwato motoci 19.

Motocin dai kamar yadda muka samu, kwamitin ya kwato su ne daga hannun tsaffin ma'aikatan hukumar nan ta kidayar al'umma ta kasa watau National Population Commission (NPopC) a turance.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel