Jihohi 12 zasu fuskanci ambaliyar ruwa – NEMA da NHISA sunyi gargadi
Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) da kuma hukumar National Hydrological Services Agencies (NHISA) sunyi gargadin cewa jihohi12 a fadin kasar zasu fuskanci ambaliyar ruwa sakamakon yawan ruwan sama.
Hukumomin biyu sun yi gargadin ne a raanar Juma’a, 7 ga watan Satumba a lokacin wani taron gaggawa na masu ruwa da aka gudanar a Abuja.

Asali: Depositphotos
Mista Clem Nze, daraktan NHISA ya lisaffo jihohin a matsayin:
1. Kogi
2. Kebbi
3. Niger
4. Kwara
5. Edo
6. Anambra
7. Rivers
8. Bayelsa
9. Delta
10. Taraba
11. Benue
12. Adamawa
Ambaliyar zai fito ta kogin Niger wato River Niger sauran jihohin kuma zasu fuskanci nasu ta kogin Benue wato River Benue kamar yadda suka yi gargadi.
KU KARANTA KUMA: Yan sanda sun sha alwashin yin maganin yan daban siyasa da masu daukar nauyinsu a Kano
Rahoton ya kara da cewa kwararru sun yi gargadin cewa ambaliyar ruwan na iya yin barna domin cewa duk alamu da suka nuna kafin ambaliyar ruwan 2012 sun fara nuna alamu.
Sunyi kiran ne domin mazauna yankunan da masu ruwa da tsaki su kwana cikin sanin halin da ake ciki.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng