2019: Ina neman kujerar Buhari ne domin na hada kan Najeriya - Saraki

2019: Ina neman kujerar Buhari ne domin na hada kan Najeriya - Saraki

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya bayyana cewa babban dalilin da yasa yake takaran kujerar shugaban kasa a 2019 shine domin ya hada kan dukkanin kabilun Najeriya a waje daya.

Saraki wadda ya ziyarci Enugu a ranar Alhamis, 6 ga waan Satumba don sanar da magoya bayan jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) kudirinsa na takaran shugaban kasa yace zai daura hadin kan kasar akan turban inganta tattalin arziki.

Mutanen jihar da mambobin PDP sun shiga ruwaan sama domin yiwa shugaban majalisar dattawan tarba tun daga filin jirgin sama na Akanu Ibiam, Enugu har zuwa sakatariyar PDP a GRA, Enugu.

2019: Ina neman kujerar Buhari ne domin na hada kan Najeriya - Saraki
2019: Ina neman kujerar Buhari ne domin na hada kan Najeriya - Saraki
Asali: Depositphotos

Saraki ya bayyana cewa Najeriya na bukatar Shugaban Kasa da zai hada kan kasar, inda ya kara da cewa dan siyasan da ya san matsalolin al’umma ne kawai zai kawo mafita da hadin kan mutane.

Ya bayyana cewa a yanzu haka yan Najeriya na fuskantar matsin rayuwa inda yawan marasa aikinyi ke karuwa sannan kuma yawanci iyalai basu samu abincin da zasu ci su koshi.

Saraki ya bukaci mutanen Enugu da na kudu maso gabas da su mara masa baya a shirye-shiryensa na chanja shugabancin kasar, inda ya kara da cewa yan Najeriya na bukatar shugaban kasar da zasuyi alfahari dashi.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Ibrahim Shekarau ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa All Progressives Congress (APC) mai mulki.

KU KARANTA KUMA: 2019: Bazan iya cutar da ku ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunku - Saraki ya yiwa APC gugar zana

Shekarau ya sanar da hukuncinsa na komawa jam’iyyar APC mai mulki bayan ganawar sirri da suka yi tare da shugaban jam’iyyar na kasa, Adams Oshiomhole.

An gudanar da ganawar sirrin ne a ranar Juma’a, 7 ga watan Satumba a jihar Kano.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel