2019: Bazan iya cutar da ku ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunku - Saraki ya yiwa APC gugar zana

2019: Bazan iya cutar da ku ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunku - Saraki ya yiwa APC gugar zana

- Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki, ya yiwa APC gugar zana, yana mai cewa ba zai cutar da jam'iyyar ba, sai dai zai kwace mulki daga hannunta a 2019

- A cikin wata sanarwa, APC ta ce yan Nigeria sun gaji da irin salon mulkin Saraki na kama karya da kuma gundurarwa, wanda babu mai son ya sake maimaitawa

- Saraki wanda ya nemi jin dalilin da ya sa APC ke masa katsalandan a lamuran siyasarsa, ya ce ba shi da wata matsala da zata kawo masa cikas a fagen shugabanci

A ci gaba da musayar zafafan kamalai tsakanin shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da jam'iyya mai mulki ta APC, jam'iyyar ta APC ta yi maraba da kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2019, karkashin jam'iyyar PDP, amma da yi masa tuni, na cewar yan Nigeria sun gaji da irin salon mulkinsa.

"Yan Nigeria sun gaji da irin salon mulkin Saraki na kama karya da kuma gundurarwa, wanda kowa ya gaji dashi, ba tare da son sake maimaitawa ba," kamar yadda jam'iyyar APC ta bayyana.

Sai dai Saraki a cikin wani martani, ya caccaki shugabancin jam'iyyar ACP, yana mai cewa jam'iyyar da shuwagabanninta sun riga ya sun tsorata da shi, tun bayan da ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin PDP, tare da shan alwashin kaucewa dukkanin tuggun da zasu kulla masa.

A cikin wata sanarwa daga hannun sakataren watsa labarai na jam'iyyar APC, Yekini Nabena, jam'iyyar ta kuma kawo batun kabilanci da ya shafi kudirin Saraki na shugabantar kasar.

2019: Bazan iya cutar da ku ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunku - Saraki ya yiwa APC gugar zana
2019: Bazan iya cutar da ku ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunku - Saraki ya yiwa APC gugar zana
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Bayan shekaru 48: A karon farko Mace ta zama shugabar ma'aikata jihar Benue

Jam'iyyar ta ce: "A karshe dai, shugaban majalisar dattijai ya bayyana kudirinsa na tsayawa takarar shugabancin kasar.

"A yayin da jam'iyyar APC, ke masa maraba da shiga sahun yan takarar shugaban kasar, tunda yana da yancin tsayawa takarar kasancewarsa dan kasa, sai dai, akwai wasu matsaloli da suka shafi nagartarsa, kwarewarsa, da kuma dabarun iya shugabantar kasa kamar Nigeria."

Sai dai jim kadan bayan fitar wannan sanarwa ta APC, a jiya Alhamis, Saraki ya saki tashi sanarwar, ta hannun mai bashi shawara na musamman kan kafofin watsa labarai, Yusuph Olaniyonu, inda ya yiwa APC gugar zana.

Sanarwar ta ce: "APC ta tsorata da ni, tun bayan da na nuna sha'awar tsayawa takara jam'iyyar ke kumfar baki, wannan alama ce karara ta tsorata, da tunanin zan samu nasara a zaben 2019. To ta kwantar da hankalinta, ta bar jin tsoro na, ba zan iya cutar da ita ba, sai dai zan kwace mulki daga hannunta cikin ruwan sanyi"

Saraki wanda ya nemi jin dalilin da ya sa APC ke masa katsalandan a lamuran siyasarsa, ya ce ba shi da wata matsala da ta shafi kwarewarsa ko gogewarsa a fagen shugabanci, kamar yadda APC da gwamnati ke ikirari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel