Oshiomole, Tinubu, Ganduje za su gana da Shekarau a yau gabanin sauya shekarsa gobe
Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress, APC, Adams Oshiomole, babban jigon jam'iyyar, Bola Tinubu, tare da wasu mambobin majalisar dokokin tarayya za su gana da tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarai, a gidansa dake Mundubawa yau Juma’a, 7 ga watan Satumba, 2018.
Jaridar Daily Nigerian ta samu rahoton cewa ganawar da daga cikin shirye-shiryen da yarjejeniya kafin sauya shekar Shekarau. An shirya zaman ne domi kara gamsar da Sardaunan Kanon muhimmanci fitarsa daga PDP.
A wata wasika da Ubale Jakada ya turawa kwamitin Shekarau, za’ayi ganawar ne a gidan Shekarau misalin karfe 10 na safe.
KU KARANTA: Kudirin Saraki na tsayawa takarar shugaban kasa, kamar almara ne - APC
Mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya bayyana a daren jiya cewa tsohon gwamnan zai yanke shawararsa na tsayawa ko fita daga PDP ranan Asabar.
Kana mai magana da yawun gwamna Ganduje, Salihu Tanko Yakassai ya jaddada hakan a wani jawabi da yayi a shafinsa na Tuwita.
Shugaban jam’iyyar APC a jihar Kano, Abdullahi Abbas, a ranan Laraba ya ce dawowan Malam Ibrahim Shekaru jam’iyyar APC na nuna cewa itace jam’iyya mafi zaman lafiya da kuma adalci.

Asali: Depositphotos
Mun kawo muku rahoton cewa Wasu na kusa da Shekarau da suka hallarci tattaunawar sunce Malam Shekarau ya nemi a bashi kujerar takarar Sanata kana a bashi damar fitar da dan takarar mataimakin gwamna a jihar Kano.
Daily Nigerian ta gano cewa Mallam Shekarau yana son ya Ganduje ya amince da Umar Maimansaleta a matsayin mataimakin gwamna amma gwamna Ganduje baiyi maraba da batun ba.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng