Yan Nigeria sun koka kan yawaitar Lalatattun N100, sun roki Shugaban kasa da CBN da a bugo sabbi
- Yan Nigeria sun koka tare da rokon shugaban kasa Muhammadu Buhari da babban bankin Nigeria (CBN), da su taimaka su buga sabbin takardun kudi
- Lalatattun N100 sun fi yaduwa a jihar Legas, inda ya ke zama abun wahala mutumya samu sabuwar takardar kudin.
- Babban abin tayar da hankalin a cewar sa shine, yadda bankuna da yan kasuwa ke kin karbar lalatattun kudaden
Kamar yadda kudaden jabu suka zama ruwan dare a tsakanin jama'a, haka lamarin ya ke a yawaitar lalatattun N100, kasancewar an tsara su ne akan takarda, wanda ke sanya su lalacewa cikin kankanin lokaci, koda kuwa mai rike da su yana matukar taka tsantsan akan ma'adanarsu.
Ya Allah wannan ne ya sa yan Nigeria kokawa, tare da yin korafi akan yadda lalatattun takardun N100 ke kokarin mamaye kasar. Da yawan mutane na ganin cewa takardar N100 na wuyar samu a kasar, idan kuwa an same su, to ko dai a same su sun rabe gida biyu an manne da salataf, ko kuma wani bangare ya cire, an dauko na wani kudin a hada su.
Lalatattun N100 sun fi yaduwa a jihar Legas, inda ya ke zama abun wahala mutumya samu sabuwar takardar kudin.
KARANTA WANNAN: Rai dangin Goro: Ambaliyar ruwa ta lakume rayukan mutane 16 a jihohin Kano da Jigawa
Wasu yan Nigeria da lamarin ya kaisu bango, sun fito fili don nuna korafinsu, tare da rokon shugaban kasa Buhari, da babban bankin Nigeria (CBN), da su taimaka su buga sabbin takardun N100 don magance karancinsu a cikin jama'a.
A cewar wani matashi, da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce: "A lokacin shugabancin Goodluck, bamu fuskanci matsalar yawaitar lalatattun kudi ba, idan har gwamnati mai ci a yanzu na son kawo canji a kasar, to ya zamar mata wajibi ta gaggauta bugo sabbin takardun kudi musamman ma N100, domin hakan na shafar talaka"
Babban abin tayar da hankalin a cewar sa shine, "yadda bankuna da yan kasuwa ke kin karbar lalatattun kudaden, sau tari sai dai mutum yayi asara, yana ji yana gani."
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng