Da wakilai za mu yi zaben fidda gwani a Kaduna – APC

Da wakilai za mu yi zaben fidda gwani a Kaduna – APC

- Jam'iyyar APC reshen Kaduna tace wakilai zata yi amfani da su wajen zaben fidda gwani

- Shugaban jam'iyyar ya bayyana dalilinsu da zabar wannan tsari

- Sanata Shehu Sani da wasu yan jam'iyyar dai sun rubutawa uwar jam'iyya korafi akan haka a baya

Duk da korafe-korafe da Sanata mai wakiltan Kaduna ta tsakinya, Shehu Sani da wasu manyan yan siyasa suka yi akan amfani da zaben fidda gwani na wakilai, a yau Alhamis, 6 ga watan Satumba jam’iyyar APC reshen jihar Kaduna ta ce shi zata gudanar.

A cewar wata sanarwa dauke das a hannun shugaban jam’iyyar Emmanuel Jekada, jam’iyyar tace wakilai zata yi amfani da su wajen zaben yan takaranta.

Jekada ya bayyana wasu hujojji da ya sa jam’iyyar ta dauki matsayin yin amfani da wakilai.

Da wakilai za mu yi zaben fidda gwani a Kaduna – APC
Da wakilai za mu yi zaben fidda gwani a Kaduna – APC
Asali: UGC

"Mun gwada yin amfani da zabe na kai tsaye wato na bai daya a zaben fidda ‘yan takara lokacin da muke zaben kananan hukumomi a jihar. Hakan ya jawo tashin hankali matuka a tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar.

KU KARANTA KUMA: Tuna-baya: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

“Bayan haka mu zabe na (Kai tsaye) na da matukar tsada. Sannan ko ta wajen daukar dawainiyar jami’an tsaro kawai za a jigata."

Ya ce uwar jam’iyyar ta aikawa hedikwatar jam’iyyar na kasa da matsayin ta.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa dan majalisa mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani akan mamayar da wasu jami’an yan sanda suka kai gidan babban jigon kasar Edwin Clark dake Abuja.

Sani wadda ya soki yan sanda a shafinsa na Twitter akan harin da ya haifar da cece-kuce a fadin kasar yace yan sanda su tafi wani wuri neman makamai maimakon kai mamaya gidan da suka san abunda zasu samu mai wuce litattafai da sauran kayayyakin aikin gida ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel