An damke matasa 41 da ake zargi luwadi a taron banbadewa a jihar Bauchi

An damke matasa 41 da ake zargi luwadi a taron banbadewa a jihar Bauchi

Hukumar yan sandan Najeriya tare gudunmuwar jami’an yan sandan farin hulla wato NSCDC sun cika hannu da akalla mutane 41 da ake zargi da luwadi a jihar Bauchi.

Kakakin hukumar yan sandan jihar, Kamal Abubakar, wanda ya tabbatar da wannan labarin ya ce hukumar ta kai karan da 37 daga cikinsu kotu.

Yace: “Duk da cewan mun samu rahoton cewa wadanda suke argi yan luwadi ne, bamu kaisu kara kotu a matsayin yan luwadi ko yan madugo bat un bamu kamasu turmi da tabarya ba. Kawai mun tuhumesu da da laifin damun jama’an unguwa ne tunda a wani taron banbadewa murnan ranan haihuwa.”

Abubakar wanda DSP ne a hukumar ya jaddada cewa hukumar ba zata gajiya ba wajen kare rayuka da dukiyan mutan jihar Bauchi.

KU KARANTA: Lokacin da Buhari ya jinjinawa tsohon Gwamnan Kano Kwankwaso

Kwamishanan harkokin addinin jihar Bauchi, Alhaji Ado Zigau, ya ce an damke matasan ne bisa ga rahoton cinne da suka samu.

Yace: “Rahoton leken asiri ya bayyana cewa wasu yan madugo da luwadi sun shirya taro a dakin taron Federal Secretariat, an tura jami’an tsaro wajen kuma suka kama su. An kaisu ofishi domin gudanar da bincike.”

A bangare guda, hukumar NSCDC ta bayyana hudu daga cikinsu, a cewar Kakakin hukumar DSC Garkuwa Adamu.

Daya daga cikin wadanda aka kama, Abubakar Adamu, ya musanta zargin da ake musu cewa su yan luwadi ne. Yace: “ Mu bay an luwadi bane kuma babu yan madugo a cikinmu. Na shirya taro ne kuma na gayyaci abokai na… Ni tela ne kuma mun bi tsarin doka wajen hayan dakin taron da aka bamu.”

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel