Idan makamai kuke nema ku tafi Sambisa – Shehu Sani ga yan sanda

Idan makamai kuke nema ku tafi Sambisa – Shehu Sani ga yan sanda

Dan majalisa mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya a majalisar dokokin kasar, Sanata Shehu Sani ya mayar da martani akan mamayar da wasu jami’an yan sanda suka kai gidan babban jigon kasar Edwin Clark dake Abuja.

Sani wadda ya soki yan sanda a shafinsa na Twitter akan harin da ya haifar da cece-kuce a fadin kasar yace yan sanda su tafi wani wuri neman makamai maimakon kai mamaya gidan da suka san abunda zasu samu mai wuce litattafai da sauran kayayyakin aikin gida ba.

“Idan kuna neman hular malafa, sandar dogarawa da litattafai ku tafi gidan Clark; idan kuna neman makamai ku tafi dajin Sambisa,” inji shi.

“Mamayar da aka kai gidan Cif EK Clarks abun korewa ne. Kamata yayi hukumomin tsaro su dunga mututunta dattijon domin sun san makomar irin hakan. Yan sanda su bashi hakuri,” cewarsa a shafin twitter a ranar 5 ga watan Satumba."

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Atiku da magoya bayansa sun mamaye hedkwatar PDP

A baya Legit.ng ta rahoto cewa babban sufeton yan sanda ya yi umurnin dakatar da jami’an yan sanda uku dake da hannu a birkice gidan Cif Edwin Clark a Abuja ba bisa ka’ida ba.

Hakan na kunshe ne a wani jawabi da aka aikewa Legit.ng a ranar Alhamis, 6 ga watan Satumba daga kakakin rundunar, ACP Jimoh Moshood.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel