An damke yan leken asirin Boko Haram cikin sansanin IDP

An damke yan leken asirin Boko Haram cikin sansanin IDP

Hukumar yan sandan jihar Borno ta bayyana cewa mutane uku daga cikin yan Boko Haram 22 da aka damke watanni biyu da suka gabata mambobin kungiyar “Daular addinin Musulunci a yankin Afrika ta yamma” ne wato ISWAP.

ISWAP wata balli daga ISIS wacce aka kafa da wasu yan tawayen Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

Wani mataimakin kwamishanan yan sanda a jihar Borno, Ahmed Bello, ya bayyana hakan ne yayin jawabi kan al’amarin tsaro a wani shirin da aka shrya a Maiduguri.

Bello, wanda ya wakilci kwamishanan yan sandan jihar, Damien Chukwu, ya ce an tabbatar da cewa daga cikin mutane 22 da aka kama watanni biyu da suka shude, akwai mambobin ISIS a cikinsu.

An damke yan leken asirin Boko Haram cikin sansanin IDP
An damke yan leken asirin Boko Haram cikin sansanin IDP
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Kamfanin Ruyi za su sanya hannun jarin $200m a Kano, Katsina, Legas da Abia bayan ganawarsu da Buhari a Sin

Ya ce yan ta’addan sun kasance suna zama a sansanin IDP ne domin leken asirin yadda abubuwa ke gudana ba tare da an farga da sub a.

“Mun kaddamar da shirye-shirye a gidajen rediyo domin wayar da kan jama’a kan lura da unguwannisu.

“Zai baku mamakin cewa wasu mutane da ke zaune cikin sansanin IDP bay an gudu hijra bane. Saboda haka idan kuka ga wani wanda baku yada da shi ba, ku kamashi saboda yan ta’addan na da wadanda ke basu rahoto.”

Ya kara da cewa damke wadannan yan ta’adda ya rage harin kunar bakin wake da ake kaiwa cikin garin Maiduguri.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel