Kanin wani dan takarar shugaban kasa a PDP zai koma APC

Kanin wani dan takarar shugaban kasa a PDP zai koma APC

- Kanin wani dan takarar shugaban kasa a PDP zai koma APC

- Yace uwar jam'iyyar zata yi biki karbar sa

- Ya zargi yayan sa da yi fatali da shi bayan ya taimake sa a 2015

Batun takarar shugabancin kasa da gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo ke yi da alama za ta fuskanci babbar cikas a yayin ake ta rade-raden cewa daya daga cikin kannen sa, watau Buhari Mohammed Dankwambo da aka fi sani da BHD, ya kammala shirin fita daga PDP ya koma APC.

Kanin wani dan takarar shugaban kasa a PDP zai koma APC
Kanin wani dan takarar shugaban kasa a PDP zai koma APC
Asali: Twitter

KU KARANTA: Kwankwaso da Ganduje sun yi kicibis a filin jirgi

Da yake zantawa da manema labarai, Alhaji Buhari Mohammed Dankwambo yace tuni ya gama yanke shawarar fita daga PDP zuwa APC din kuma yana jiran umurnin uwar jam'iyya ne kawai da zata saka ranar karbar sa da dumbin magoya bayan sa.

Legit.ng ta samu cewa shi dai Buhari Dankwambo ya zargi yayan na sa ne da yin fatali da shi bayan ya kashe masa makudan kudade wajen nemar masa tazarce a shekarar 2015.

Masana siyasa dai na ganin idan har kanin na gwamnan ya fita daga PDP to fa lallai hakan zai zama tamkar babban nakasu gareshi.

A wani labarin kuma, Jam'iyya ma mulki a Najeriya ta All Progressives Congress (APC) shiyyar jihar Ondo tayi fatali da tsarin zaben fitar da gwani na kato-bayan-kato a ranar Larabar da ta shude biyo bayan wani zama da jiga-jigan ta suka yi a garin Akure, babban birnin jihar.

Da yake yin jawabi ga manema labarai jim kadan bayan kammala taron na masu ruwa da tsakin jam'iyyar a jihar, Satana Tayo Alasoadura dake wakiltar mazabar shiyyar jihar ta tsakiya ya ce sun yanke shawarar ne bayan doguwar muhawara.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel