Hukumar NNPC tayi gamsasshen bayani game da labarin daukar ma'aikatan ta

Hukumar NNPC tayi gamsasshen bayani game da labarin daukar ma'aikatan ta

- Hukumar NNPC tayi gamsasshen bayani game da labarin daukar ma'aikatan ta

- Tace yan damfara ne ke anfani da sunan hukumar

- Ta kuma ce duk wanda ya yadda aka damfare shi to ya kuka da kansa

Mahukunta a rukunin kamfanonin albarkatun mai na kasa watau Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC) sun fitar da sanarwa dauke da gamsasshen bayani game da labarin daukar ma'aikata da ake ta rade-raden tana yi.

Hukumar NNPC tayi gamsasshen bayani game da labarin daukar ma'aikatan ta
Hukumar NNPC tayi gamsasshen bayani game da labarin daukar ma'aikatan ta
Asali: UGC

KU KARANTA: Wani malami yayi kaca-kaca da masoyan Buhari

Shugaban sashen hulda da jama'a na hukumar, Mista Ndu Ughamadu a cikin wata sanarwa da ya fitar ya kuma rabawa manema labarai, ya bayyana cewa duk labarin kanzon kurege ne batun daukar aikin da ake ta yamadidi da shi musamman ma a zaurukan sada zumunta.

Legit.ng ta samu cewa Mista Ndu ya fito karara ya bayayyana cewa dukkan masu cewa ana daukar aiki a ma'aikatar 'yan damfara ne kuma dukkan wanda ya yadda da su ko ya fada tarkon su to lallai ya kuka da kansa.

Haka zalika sai kuma ya shawarci al'ummar kasar da su taimakawa jami'an tsaron da abun ya shafa idan har suka ci karo da irin 'yan damfarar domin hukunta su.

A wani labarin kuma, Wasu matasa a karkashin inuwar kungiyar 'Zauren Olanrewaju Oba' dake a jihar Kwara, shiyyar Arewa ta tsakiya sun sha alwashin gudanar da gangamin matasa miliyan daya don nuna goyon bayan su ga dan takarar shugaban kasar Najeriya, Sanata Abubakar Bukola Saraki.

Shugaban matasan Olanrewaju Oba yace gangamin ya zama dole ne a gare su musamman ma duba da irin kyawawan kudurorin sa ga al'ummar Najeriya tun sadda yake gwamna a jihar ta Kwara da ma shugaban majalisar dattawa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel