Kishin-Kishin: Shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba ya korar wasu a gwamnatin sa

Kishin-Kishin: Shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba ya korar wasu a gwamnatin sa

- Shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba ya korar wasu a gwamnatin sa

- Ministan Shari'a Abubakar Malami da Dakta Mai kanti Baru na cikin wadanda zai kora

- Ana sa ran ya kore su kafin lokacin zaben 2019

A wani labarin da muka samu daga jaridar Vanguard ya shaida mana cewa yanzu haka Shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba daga manyan aminan sa wajen ganin lallai ya kori wasu daga cikin jami'an gwamnatin sa kafin zaben 2019.

Kishin-Kishin: Shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba ya korar wasu a gwamnatin sa
Kishin-Kishin: Shugaba Buhari na fuskantar matsin lamba ya korar wasu a gwamnatin sa
Asali: Facebook

KU KARANTA: Atiku ya fadi wasu munanan halayen Buhari

Wasu daga cikin wadanda ake so Shugaban kasar ya kora kamar yadda muka samu sun hada da Ministan Shari'a Abubakar Malami, SAN da shugaban rukunin kamfanin albarkatun man fetur na kasa wata Nigerian National Petroleum Corporation (NNPC', Dakta Maikanti Baru.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa sauran sun hada da Shugaban gidauniyar kasa da zuba jari watau Nigerian Sovereign Investment Fund (NSIA) Mista Uche Orji da ma wasu sauran daban.

An ce dai ana so a canja su ne domin a samu damar nada wasu sabbi masu jini a jika kuma 'yan siyasa wadanda za su taimakawa Shugaban kasar wajen sake lashe zaben sa a 2019.

A wani labarin kuma, Fitaccen dan majalisar dattawan Najeriya dake wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani a ranar Talatar da ta gabata ya jagoranci wasu 'yan jam'iyyar APC zuwa hedikwatar ta kai kara.

Kamar dai yadda muka samu, Sanata Shehu Sani da sauran 'yan APC sun je ne a wajen uwar jam'iyyar inda suka bukaci cewa ta tilastawa jam'iyyar a matakin jihar ta Kaduna gudanar da zabukan fitar da gwani na tsarin kato-bayan-kato.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel