PDP ta tabbatar da tattaunawa da gwamnonin APC 6 da yan majalisa 27

PDP ta tabbatar da tattaunawa da gwamnonin APC 6 da yan majalisa 27

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba ta tabbatar da cewar ta kammala tattaunawa da gwamnonin jiha da yan majalisar dokokin kasar da aka zaba a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) gabannin sauya shekarsu zuwa PDP.

A cewar wata sanarwa daga hannun Kola Ologbondiyan, babban sakataren jam’iyyar a Abuja, PDP tace tuni ta kammala tattaunawa tare da wasu gwamnonin APC shida da mambobin majalisar dokokin kasar 27 wadda suka tuntubi jama’a sannan suka samu goyon bayan mazabunsu kan su koma PDP kafin zaben 2019.

Sanarwan ya bayyana cewa ana tattaunawa akan shugabancin jam’iyyar a wadannan jihohi da mazabun za’a kuma kammala komai nan da yan kwanaki inda bayan nan gwamnonin da yan majalisa zasu sanar da sauya shekarsu zuwa PDP.

PDP ta tabbatar da tattaunawa da gwamnonin APC 6 da yan majalisa 27
PDP ta tabbatar da tattaunawa da gwamnonin APC 6 da yan majalisa 27
Asali: Depositphotos

Jam’iyyar ta bayar da tabbacin cewa abubuwa zasu daidaita kwanan nan.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yanki fam din nuna ra’ayin tsayawa takaran kujerar shuaban kasa a zabe mai zuwa karkashin jam’iyyarsa All Progressives Congress (APC) mai mulki.

KU KARANTA KUMA: 2019: Tawagar yakin neman zaben Saraki sun isa yankunan arewa maso yamma da arewa maso gabas

Kungiyar magoya bayan shugaban kasar mai suna Nigerian Consolidation Ambassadors Network ce ta siya fam din a madadin shugaban kasar a ranar Laraba, 5 ga watan Satumba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng