Banbarakwai: Za'ayi gagarumin taron manyan malaman kiristoci a Sakoto birnin Shehu

Banbarakwai: Za'ayi gagarumin taron manyan malaman kiristoci a Sakoto birnin Shehu

- Za'ayi gagarumin taron manyan malaman kiristoci a Sakoto birnin Shehu

- Bishop Matthew Kukah ne ya sanar da hakan

Akalla manyan malaman addinin kirista da suka kai matsayin bishof-bishof su saba'in da biyar aka sa ran za su taru a garin Sokoto mai dumbin tarihi kuma daular musulunci dake a shiyyar Arewa ta yamma daga Shidda ga watan Satumba domin gabatar da wani gagarumin taron karawa juna sani.

Banbarakwai: Za'ayi gagarumin taron manyan malaman kiristoci a Sakoto birnin Shehu
Banbarakwai: Za'ayi gagarumin taron manyan malaman kiristoci a Sakoto birnin Shehu
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wani gwamna ya roki Buhari ya yafewa barayin Najeriya

Daya daga cikin mahalarta taron kuma mai masaukin baki Bishop Matthew Kukah dake zaman shugaban malaman addinin kiristan na kabilar katolika shine ya sanar da hakan a cikin wata sanarwar manema labarai da ya fitar.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa Bishop Matthew Kukah ya ce taron da za su gudanar zai ta'allaka be wajen karawa junan su sani tare kuma da tattaunawa akan yadda za su tunkari wasu daga cikin matsalolin da suka addabi kasar.

A wani labarin kuma, Daya daga cikin manyan malaman addinan kirista a kasar nan kuma shugaban rukunin majami'un Mount Zion Faith Global Liberation Ministry Inc.( a.k.a. By Fire By Fire) da ke a garin Nnewi, jihar Anambra mai suna Bishop Abraham Udeh ya yi kaca-kaca da masoya Muhammadu Buhari.

Bishop din wanda a jiya ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa dukkan masu son Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zarce to lallai shi babban makiyin demokradiyya ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel