Tsugene bata kare ba: Sanata Shehu Sani da wasu manyan 'yan APC sun kai kara gaban uwar jam'iyya
- Sanata Shehu Sani da wasu manyan 'yan APC sun kai kara gaban uwar jam'iyya
- Yace shi da su duka basu yadda da zaben fitar da gwani na deliget ba
- Yace cin hanci da rashawa ne kawai tattare da hakan
Fitaccen dan majalisar dattawan Najeriya dake wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani a ranar Talatar da ta gabata ya jagoranci wasu 'yan jam'iyyar APC zuwa hedikwatar ta kai kara.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Kwankwaso ya kwace PDP a jihar Kano
Kamar dai yadda muka samu, Sanata Shehu Sani da sauran 'yan APC sun je ne a wajen uwar jam'iyyar inda suka bukaci cewa ta tilastawa jam'iyyar a matakin jihar ta Kaduna gudanar da zabukan fitar da gwani na tsarin kato-bayan-kato.
Legit.ng ta samu cewa a lokacin da suke yi wa manema labarai jawabi a wajen kai takardar karar, sun bayyana cewa ya kamata jam'iyyar ta sa baki don ganin an kori cin hancin da kan dabaibaye tsarin zabukan fitar da gwani na 'yan takara a zabukan 2019 masu zuwa.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a satukan da suka gabata ne dai kwamitin zartaswa na jam'iyyar ya fitar da tsarin gudanar da zabukan fitar da gwani na kato-bayan-kato inda kuma wasu gwamnoni suka nuna rashin amincewar su da hakan.
A wani labarin kuma, Daya daga cikin manyan malaman addinan kirista a kasar nan kuma shugaban rukunin majami'un Mount Zion Faith Global Liberation Ministry Inc.( a.k.a. By Fire By Fire) da ke a garin Nnewi, jihar Anambra mai suna Bishop Abraham Udeh ya yi kaca-kaca da masoya Muhammadu Buhari.
Bishop din wanda a jiya ya zanta da manema labarai, ya bayyana cewa dukkan masu son Shugaban kasar Muhammadu Buhari ya zarce to lallai shi babban makiyin demokradiyya ne.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng