Miji da mata sun sayar da yaronsu daya tilo N180,000 a garin Calabar

Miji da mata sun sayar da yaronsu daya tilo N180,000 a garin Calabar

Wani magidanci mai suna, Mr Daniel Bassey, da matarsa, Magdalene, sun shiga hannun hukuma da laifin sayar da yaronsu kudi N180,000 ga wani dillali a garin Fatakwal, jihar Ribas.

Yayinda ake gurfanar da su tare da wasu mutane 78 da suka aikata wasu laifuka a hedkwatar hukumar da ke Calabar, jihar Cross River, kwamishanan yan sandan jihar, Mr Hafiz Inuwa, yace an damkesu ne ranan 23 ga watan Yuli 2018 a Calabar.

Inuwa yace mahaifiyar ce ta kawo kara ofishin hukumar yan sanda da ke Efut cewa mijinta ya dauki dansu daya tilo, Moses Bassey, zuwa wurin wani a Fatakwal kuma ya kawo kudin gida.

KU KARANTA: Kungiya tayi karar Saraki da Akpabio kan sauyin sheka

Yace: “A ranan 23 ga watan Yuli 2018, wata mata mai suna Magdalene Bassey, taa kawo kara hedkwatan yan sandan Efut dake Calabar cewa mijinta, Mr Daniel Bassey, ya dauki yaronsu zuwa wurin wani mutum a Fatakwal.”

“Ba tare da bata lokaci ba, jami’an yan sanda suka laluboshi. A yayin bincike, ya bayyana cewa da sanin matarshi hakan ya faru. A yanzu suna hannun hukumar domin sanin abinda yasa sukayi hakan da kuma matakin da za’a dauka a kansu.”

Miji da mata sun sayar da yaronsu daya tilo N180,000 a garin Calabar
Miji da mata sun sayar da yaronsu daya tilo N180,000 a garin Calabar
Asali: Depositphotos

Ya ce hukumar na kokarin yadda za’a ceto dan yaron.

A yayin wani hira da manema labarau ranan Talata, Daniel Bassey, ya bayyana abin ya faru kuma cewa za’a bada yaron ne matsayin jingina domin kudi N180,000 na biyan kudin haya.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel