Matasa 1,086 sun kamu da cutar Kanjamau a jihar Nasarawa

Matasa 1,086 sun kamu da cutar Kanjamau a jihar Nasarawa

- An siffata Yawan zinace-zinace matsayin babban musababbin yaduwar cutan Kanjamau

- Matan Najeriya sun fi kamuwa da cutan fiye da maza

Kimanin matasa 1,086 cikin 75, 435 masu shekaru tsakanin 14 da 19 ke fama da cutan kanjamau wanda aka tabbatar a jihar Nasarawa, Arewa maso tsakiyar Najeriya.

Diraktan hukumar dakile cutan Kanjamau a jihar Nasarawa, Dr Ruth Adabe, ta bayyana hakan ne a ranan Lahadi, 2 ga watan Satumba a wani waksho na kwana daya.

Wannan waksho da kungiyar tallafin yara da majalisar dinkin duniya ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar wayar da kan yan Najeriya wato National Orientation Agency, a karamar hukumar Keffi, jihar Nasarawa.

KU KARANTA: Kungiya tayi karar Saraki da Akpabio kan sauyin sheka

Yayinda take jawabi a taron, Adabe, wacce Dr. Peter Attah ya wakilta ta bada shawarwari kan yadda za’a kawo karshen cutan Kanjamau. Daga ciki akwai gina cibiyoyin matasa, gwajin cutar kanjamau da sauransu.

Ta daura laifin wannan abu kan matasa domin sanya kansu cikin haduran wanna cuta da wasu cututtuka da akan kama ta hanyar jima’i.

Tace: “A shekarar 2016, kimanin matasa yan shekaru kasa da ashirin 240,000 ke fama da cutan, wanda ya sanya kashi 7 cikin matasan Najeriya na kame da cutan.”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel