Tsumagiyar kan hanya: Rundunar yan sanda ta kai sumame a gidan Edwin Clark na Abuja

Tsumagiyar kan hanya: Rundunar yan sanda ta kai sumame a gidan Edwin Clark na Abuja

Rahotannin da ke zuwa ma Legit.ng na nuni na cewa rundunar yan sanda a yau Talata ta kai sumame a gidan kwamishinan kasa kan yada labarai, kuma shugaban yankin Kudu maso Kudu, Chief Edwin Clark.

Rundunar wacce ta gudana da bincike daki bayan daki na gidan mai fada ajin, sun yi ikirarin cewa sun kai sumame gidan ne don binciken wasu makamai da aka yi zargin an boye su a cikin gidan.

Jami'an tsaron sun isa gidan Chief Clark da ke Asokoro da misalin karfe 1:30 na rana, inda suka bar gidan da misalin karfe 2:30 na rana.

Yanzu yanzu: Rundunar yan sanda ta kai sumame a gidan Edwin Clark da ke Abuja
Yanzu yanzu: Rundunar yan sanda ta kai sumame a gidan Edwin Clark da ke Abuja
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: APC ta bayyana dalilin da ya sa ta zabi yin kato bayan kato a zaben fitar da gwani

Sai dai har zuwa lokacin da suka kammala binciken, ba su samu wasu makamai ko kayan laifi ba.

A cewar rundunar, sun kai sumame gidan ne bisa umarnin Sifeta Janar na rundunar yan sanda ta kasa, Ibrahim Idris.

Cikakken labarin na zuwa...

A WANI LABARIN:

A baya bayan nan Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar 'yan sanda ta cafke wasu miyagun mutane uku da suka yi garkuwa da wani kankanin yaro dan shekara hudu a cikin tantagwaryar birnin jihar Kano dake Arewacin Najeriya.

Kakakin hukumar 'yan sanda na jihar, DSP Magaji Musa Majiya, shine ya bayyana hakan yayin ganawar sa da manema labarai cikin birnin jihar a ranar Litinin din da ta gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel