Shugaban Cocin Anglica: Mummunar dabi'ar Luwadi da Madigo na durkusar da ci gaban Nigeria

Shugaban Cocin Anglica: Mummunar dabi'ar Luwadi da Madigo na durkusar da ci gaban Nigeria

- Shugaban Cocin Anglican na Nigeria, a bayyana wannan mummunar dabi'ar da zama silar durkushewar ci gaban kasar.

- Mr. Nicholas Okoh, ya ce dukkanin abubuwan da ke faruwa a Nigeria na faruwa ne sakamakon dabi'un da ake koyo daga kasashen ketare.

- A shekara ta 2014, an kaddamar da dokar SSMPA data haramta auren jinsi, inda aka samar da hukuncin shekaru 14 a gidan kaso ga duk wanda ya karya dokar.

Sanin kowa ne, dabi'ar madigo da luwadi sun zamo ruwan dare a kasashen duniya, ciki kuwa harda kasar Nigeria. Ya Allah wannan dalilin ne ya sa shugaban Cocin Aglican ta Nigeria, Nicholas Okoh, ya bayyana wannan mummunar dabi'ar da zama silar durkushewar ci gaban kasar.

Okoh, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin Labarai na NAN a ranar Talata a Abuja, ya ce: "Aikata luwadi wani aikine da ya samo asali daga mummunar wayewar zamani da al'adun jahilan farko, wanda ya zama wajibi a tashi tsaye a yake shi don kare makomar yaran gobe.

"Dabi'ar luwadi na kawo koma baya ga ci gaban kasar nan, don haka bai kamata a ce ana aikata irin wannan mummunar dabi'ar a Nigeria ba."

Ya ci gaba da cewa: "Ya zama wajibi mu duba zuwan kafar watsa labarai ta tauraruwar dan Adam da idon basira, hakika zuwan tashoshin kasashen waje a tauraruwar da muke kunnawa muna kallo a gidajenmu, ta taimaka wajen gurbatar da tarbiya da al'adar al'umma, harma da shafar addini da mutuncin jama'a.

KARANTA WANNAN: A matsayina na likita, zan iya bada tabbacin cewa Buhari ya fi kashi 80 na yan Nigeria koshin lafiya - Ngige

Shugaban Cocin Anglica: Mummunar dabi'ar Luwadi da Madigo na durkusar da ci gaban Nigeria
Shugaban Cocin Anglica: Mummunar dabi'ar Luwadi da Madigo na durkusar da ci gaban Nigeria
Asali: Depositphotos

"Dukkanin abubuwan da ke faruwa a Nigeria na faruwa ne sakamakon dabi'un da ake koyo daga kasashen ketare. A yayin da mutane ke kaura daga kauye zuwa birane, sukan wurgar da koyarwar iyaye, shuwagabanni da mahukuntansu, tare da daukar wasu munanan halaye su dora ma kansu." a cewar sa." a cewarsa.

A rahoton da wani bincike da aka gabatar 2017, hukumar kididdiga ta NOIPolls, ta bayyana cewa ana ci gaba da samun karuwar mutanen da ke shiga harkar luwadi da madigo a Nigeria.

A mulkin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, an kaddamar da dokar da ta hana auren jinsi daya (SSMPA) ta 2014.

Dokar SSMPA ta haramta aure tsakanin namiji da namiji, mace da mace, da kuma haramta kafa wata kungiya ta masu mu'amala da jinsi daya, inda dokar ta samar da hukuncin shekaru 14 a gidan kaso, ga dukkanin wanda aka kama da karya dokar.

KARANTA WANNAN:

Tun daga wancan lokaci, an ci gaba da samun shari'o'i akan laifin aikata Madigo da luwadi a kasar.

A wannan gwamnati ta shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jaddada kudirinsa na dorewar wannan doka ta SSMPA, a lokacin da ya kai ziyarar kwanaki hudu kasar Amurka, a watan Yulin shekara ta 2015.

Ya ce Nigeria ba zata lamunci matsin lamba daga kasar Amurka ko wata kasa daga Yamma ba, don halasta auren jinsi a kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel