Yan takaran shugaban kasan PDP: Rikici ya kunno kai tsakanin wadanda suka dawo daga APC da wadanda suka dade a jam’iyyar

Yan takaran shugaban kasan PDP: Rikici ya kunno kai tsakanin wadanda suka dawo daga APC da wadanda suka dade a jam’iyyar

Wasu yan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP, wadanda suka kasance a cikin jam’iyyar tun shekarar 2014 sun yi gargadi ga shugabannin jam’iyyar kan baiwa wadanda suka dawo jam’iyyar bayan sun fita a 2014 fifiko akansu.

Yayinda suke wannan gargadi, sun bayyana cewa wadanda suka ki sauya sheka a 2014 ne suka rike jam’iyyar lokacin da wasu suka fice kuma suka taimaka aka kayar da jam’iyyar a shekaran 2015, saboda haka, su ya kamata fifita ba baki ba.

Shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki; tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; gwamna Aminu Waziri Tambuwal, da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, na daga cikin wadanda suka dawo jam’iyyar daga APC.

KU KARANTA: Rawar da Osinbajo ta taka wajen dawowan Shekarau APC

Komawarsu APC ya taimaka matuka wajen nasarar da shugaba Muhammadu Buhari ya samu a shekaran 2015.

Yayinda ake shirye-shiryen zaben fitar da gwanin jam’iyyar PDP, mutane biyar daga cikin yan takaran shugaban kasan da basu taba sauya sheka ba sun hada baki domin hada kawunansu wajen tabbatar da cewa daya daga cikinsu ne zai samu nasara.

Yan takaran shugaban kasan PDP: Rikici ya kunno kai tsakanin wadanda suka dawo daga APC da wadanda suka dade a jam’iyyar
Yan takaran shugaban kasan PDP: Rikici ya kunno kai tsakanin wadanda suka dawo daga APC da wadanda suka dade a jam’iyyar
Asali: Twitter

Ganawar game da wata majiya mai karfi, za’ayi ne domin jawo hankalin ‘deleget’ da kwamitin gudanarwan jam’iyyar kan yadda za’a zabi mutum daya wanda bai bata sauya sheka ba daga cikin yan takaran jam’iyyar 13.

Tsohon shugaban jam’iyyar, Ahmed Makarfi; tsohon minister, Tanimu Turaki; tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido; tsohon gwanan jihar Plateau, Jonah Jang; gwamnan jihar Gombe, Ibrahim Dakwambo; za su gana a Abuja wannan mako.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel