Yanzu-yanzu: Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC

Yanzu-yanzu: Malam Ibrahim Shekarau ya koma APC

- Babban jigon jam'iyyar PDP, Ibrahim Shekarau ya fia daga jam'iyyar PDP

- Ya bayyana cewa zuwan Kwankwaso ya kawo musu matsala a jam'iyyar

Tsohon gwamnan jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya sauya sheka daga jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP) to All Progressive Congress (APC).

Tabbatar da wannan labari ga jaridar Daily Trust da safen nan, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya'u Sule, ya bayyana cewa tsohon gwaman ya yanke shawaran fita daga jam'iyyar ne bayan muhawara tsakaninsa da mabiyansa.

Sule yace: "Ina tabbatar muku da cewa Shekarau ya yanke shawaran sauya sheka daga PDP zuwa APC bisa ga rashin adalci da akayi masa da mabiyansa da shugabancin PDP tayi."

Maigidana ya gana da gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje, a Abuja jiya kuma an yanke dukkan shawaran komawa APC. Zai gana da dukkan masu ruwa da tsaki a Kano domin bayyana sauya shekarsa ga jama'a."

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun sace wani babban malamin addini a Najeriya

Sule ya kara da cewa babu yadda zai yiwu su cigaba da kasancewa cikin PDP dubi ga irin yadda shugabancin jam'iyyar ta kasa ta karkata kan Kwankwaso sabanin sauran shugabannin PDP a jihar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel