Shuwagabannin duniya na jerin gwano don ganawa da Buhari duk da Trump ya kirashi 'maras tagomashi'

Shuwagabannin duniya na jerin gwano don ganawa da Buhari duk da Trump ya kirashi 'maras tagomashi'

- Fadar shugaban kasa ta ce kalaman batancin da Trump yayi akan Buhari ba su yi tasiri ba a dangantakarsa da sauran shuwagabannin kasashen duniya

- Fadar shugaban kasa ta kara da cewa shuwagabannin duniya ne ke jerin gwano don ganawa da Buhari duk da kalaman Trump

- Wannan sanarwa ta biyo bayan ziyarar da shugabar Jamus, Angela Markel da kuma Firan Minista, Theresa May, suka kawo Nigeria

Fadar shugaban kasa kasa a ranar asabar, 1 ga watan Satumba, ta ce munanan kalaman da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi, na kiran shugaban kasa Muhammadu Buhari da "Maras Tagomashi", bai yi wani tasiri a kan shugaban kasar ba, la'akari da yadda shuwagabannin duniya ke jerin gwanon ganawa da shi.

Idan za'a tuna, Legit.ng ta ruwaito cewa Shugaban kasa Buhari ya gana da shugabar Jamus, Angela Markel, a ranar Juma'a, 31 ga watan Augusta.

Ziyarar da Merkel ta kawo fadar shugaban kasa da ke Abuja, ta zo ne kasa da awanni 24 da ganawar shugaba Buhari da Firan Ministar Burtaniya, Theresa May.

KARANTA WANNAN: PDP ta bayyana dalilin tilasta Saraki, Tambuwal, da sauransu sa hannu a takardar rantsuwa

Babban mai tallafawa shugaban kasar kan watsa labarai da kafofin sadarwa, Garba Shehu, a lokacin da ya ke maida martani kan kalamin da Trump ya yi, ya ce sauran shuwagabannin duniya na son ganawa da Buhari.

Buhari a lokacin daya isa birnin Beinjing, kasar Sin
Buhari a lokacin daya isa birnin Beinjing, kasar Sin
Asali: Twitter

Kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito, Shehu ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Beijing, China, inda yake daya daga cikin yan rakiyar shugaba Buhari a ziyarar da yakai kasar, tare da uwar gidan shugaban kasar da kuma wasu ministoci na kasar.

Ya ce: "Kamar dai yadda tsarinmu yake, mun ce ba zamu maida raddi ga shugaban kasar Amurka ba, sai dai, wani abu da kowa ya kamata ya sani shine, shuwagabannin duniya ne ke jerin gwano don ganawa da Buhari, hakan na nuni da cewa, akwai wani abu da shuwagabannin duniya suke so dangane da Buhari da kuma yadda ya mayar da kasar.

"A lokutan baya, mun shiga wani mawuyacin hali da shuwagabannin kasashen duniya ba sa iya zuwa ganawa da shuwagabanninmu, amma komai ya canja a cikin shekaru uku" a cewarsa.

Haka zalika Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau asabar 1 ga watan Satumba, ya isa birnin Beijing, kasar Sin, don halartar taron hadin guiwar Sin da kasashen Afrika (FOCAC2018) karo na 7.

Ana sa ran gudanar da taron mai taken "Samar da hanyoyin bunkasa hadin guiwar kasar Sin da kasashen Afrika" a tsakanin kwanaki biyu, daga 3 ga watan Satumba zuwa 4 ga wata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel