Shirin yaki: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi

Shirin yaki: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi

Rahotanni sun fallasa kasar Iran a matsayin kasar dake taimaka ma yan Shi’a da makamai don sun kaddamar da yaki a kasar Iraqi da sauran kasashen dake hamayya dasu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito kasar Iran na cigaba da karfafa mayakan yan shia dake kasar Iraqi mai suna Quds da makaman kare dangi watau nukiliya don su kare kansu tare da kai ma duk wata kasar dake yaki dasu hari.

KU KARANTA: Labari cikin hotuna: Haduwar Buhari da Angela Merkel shugaban kasar Jamus a Villa

Wani hadakar jami’an gwamnatin kasar Iran guda uku, jami’a leken asiri na kasar Iraqi da wasu jami’an kasashen turai ne ta bayyana haka, inda tace a yanzu haka Iran ta aika da makaman nukiliya masu kananan zango ga yan shi’ar kasar Iraqi a watannin da suka gabata.

Shirin yaki: An fallasa kasar dake taimaka ma yan shia da makaman kare dangi
Makaman kare dangi
Asali: Depositphotos

Haka zalika wasu jami’an leken asiri guda biyar sun tabbatar da cewar Iran na taimaka ma yan shi’an Iraqi da kayan aiki domin su fara kera makamansu da kansu. “Hikimar yin haka shine don Iran ta samu tufun dafawa idan har an kai mata hari.

“Nukilyan da ta baiwa yan shi’an basu dayawa, basu wuce dozin daya ba, amma zasu iya kara yawansu idan bukatar haka ya taso.” Inji wani jami’in kasar Iran.

A baya kasar Iran ta sha yin ikirarin cewa makaman nukiliya da take kerawa zata yi amfani dasu ne kawai idan an tabata, amma sai ga shi da aka tambayi manyan jami’an kasar game da wannan batu sai suka zuke, suka ki cewa uffan.

Daga cikin makaman da yan shi’an kasar Iraqi suka samu akwai wasu nukiliyoyi masu suna Zelzal, Fateh-110, da Zolfaqar wanda zasu iya kai nisan kilomita 200 zuwa 700, wanda hakan ya sanya kasashen adawar Iran Isara’ila da Saudiyya cikin wannan zango.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel