Dandalin Kannywood: An yi sabuwar zazzafar jaruma a masana'antar fim

Dandalin Kannywood: An yi sabuwar zazzafar jaruma a masana'antar fim

- An yi sabuwar zazzafar jaruma a masana'antar fim

- Jarumar sunan ta Asiya Ahmad

- Kanwar tsohuwar jaruma Samira Ahmad ce

Ga dukkan masu bibiyar harkokin fina-finan Hausa sau da kafa, za su fahimci cewar masana'antar ta yi sabuwar bakuwar jaruma kuma kyakkyawa da ake tunanin nan ba da dadewa ba za'a fara damawa da ita sosai a harkar.

Dandalin Kannywood: An yi sabuwar zazzafar jaruma a masana'antar fim
Dandalin Kannywood: An yi sabuwar zazzafar jaruma a masana'antar fim
Asali: Twitter

KU KARANTA: Wani malamin izala ya cinye kudin masallaci a Kano

Wannan dai ba kowa bace ba face Asiya Ahmad dake zaman kanwa ga tsohuwar fitacciyar jaruma Samira Ahmad wacce ta bar harkar bayan auren da tayi a shekarun baya da mawaki T. Y. Shaba.

Legit.ng ta samu cewa fitacciyar jarumar masu sharhi akan al'amurran yau da kullum na ganin cewa ta shigo masana'antar ne da kafar dama musamman ma saboda kyawun ta wanda ya sa masu shirya fina-finan ke ta rige-rige wajen saka ta a fim din su.

Mun samu cewa fitaccen kamfanin nan Ab-Nur na hadin gwuiwa tsakanin Abdul Amart Maikwashewa da Nura M. Inuwa ne ya fara yunkurin saka jarumar a wani fim din su mai suna Ranar Aure na kafin daga baya likafa tayi gaba.

Ita dai harkar fina-finan Hausa tana fuskantar kyama da tsangwama daga al'umma da kuma malamai da suke zargin tana bata tarbiyyar al'umma, zargin da su kuma masu shirya fim din suke karyatawa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel