World Cup 2018: FIFA ta jinjinawa kungiyar Super Eagles ta Nigeria

World Cup 2018: FIFA ta jinjinawa kungiyar Super Eagles ta Nigeria

- Babbar hukumar dake kula da kwallon kafa ta duniya FIFA ta jinjinawa Super Eagles bisa kwazon da suka nuna a gasar kwallon kafa ta duniya na wannan shekarar

- Shugaban hukumar, Mr. Gianni ya yi wannan jinjinar a wata wasika, yana mai cewa ya kalli wasan Nigeria da wasu kasashe biyu

- Ya ce Nigeria na da kyakkyawar makoma a nan gaba la'akari da irin kwazon da ta nuna a wasanninta

Shugaban babbar hukumar kula da kwallon kafa ta duniya (FIFA), Mr. Gianni Infantino, ya jinjinawa kungiyar kwallon kafa ta Nigeria, Super Eagles, mai horas da yan wasa Gernot Rohr, ma'aikatan kungiyar, jami'ai dama daukacin masoya, bisa kwazon da suka nuna a gasar kwallon kafa ta duniya na wannan shekarar da aka buga a Rasha.

A cikin wata sanarwa da ya aikawa shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Nigeria NFF, Amaju Pinnic a ranar alhamis, Infantino ya ce: "Zan yi amfani da wannan damar, wajen nuna tsantsar godiyarmu ga kungiyar kwallon kafa ta kasarku, a shiga gasar cin kofin kwallo ta duniya karo na 21, wanda hukumar FIFA ta shirya.

"Gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya a wannan shekarar, gasa ce da tarihi ba zai manta da ita ba, kuma babban tarihin shine kasamcewar Super Eagles ta samu damar shiga gasar, wanda shine karo na 6 da kungiyar ta buga gasar.

World Cup 2018: FIFA ta jinjinawa kungiyar Super Eagles ta Nigeria
World Cup 2018: FIFA ta jinjinawa kungiyar Super Eagles ta Nigeria
Asali: Depositphotos

KARANTA WANNAN: Sarkin Kano ya nemi a rika damawa da Almajirai a cikin harkokin boko a Nigeria

"Hakika ina cike da farin ciki, zan kuma iya bugun kirji akan hakan, domin na halarci wasanni biyu da kuka buga tsakaninku da kasar Croatia da Iceland. Don Allah ka isar min da sakon bangajiyata ga duk wanda ya bada gudunmowarsa, musamman 'yan wasa da mai horas da su, Gernot Rohr, da jami'ai, ma'aikata da kuma uwa uba masoyan kungiyar.

"Irin wannan nasara bata samuwa sai idan anyi aiki tukuri, amfani da kwarewa da kuma bin dokokin da aka gindaya, hadi da nuna sha'awar buga wasan. Irin wannan namijin kokari da Super Eagles ta nuna, ya tabbatar da cewa akwai kyakkyawar makoma ga nasarar kungiyar a nan gaba"

Idan ba'a manta ba, Legit.ng ta ruwaito cewa Nigeria ta fice daga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniyar ne bayan da ta sha kashi da ci 2-1 a hannun Argentina, wasan da aka kyautata zaton inda Nigeria ta yi nasara, zai bada damar zuwa zagayen karshe a rukunin da take.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng