Jiragen ruwa 13 yanzu haka suna ta sauke kayan abinci da fetur a gabar tekun Najeriya

Jiragen ruwa 13 yanzu haka suna ta sauke kayan abinci da fetur a gabar tekun Najeriya

- Jirage 13 sun kawo kayan masarufi da fetur a Najeriya

- Yanzu haka jiragen na Legas ana sauke kayan su

- Jirage 4 cikin 13 din na dauke ne da man fetur

Labarin da muke samu daga majiyoyin mu dai yanzu haka sun tabbatar mana da cewa akalla jiragen ruwa goma sha ukku ne suke sauke kayayyakin masarufi da man fetur a gabar tekun Najeriya a tashar jirgin ruwan dake a Apapa, jihar Legas.

Jiragen ruwa 13 yanzu haka suna ta sauke kayan abinci da fetur a gabar tekun Najeriya
Jiragen ruwa 13 yanzu haka suna ta sauke kayan abinci da fetur a gabar tekun Najeriya
Asali: UGC

KU KARANTA: An gano kifin gwangwani 2 masu guba a Najeriya

Majiyar mu ta kamfanin dillacin labarai na Najeriya ya sanar mana da cewa jirage hudu daga cikin sha ukun man fetur ne suke dauke da shi.

Legit.ng ta samu haka zalika cewa sauran jiragen tara kuma na dauke ne da kayayyakin masarufin da suka hada da na ci kamar alkama da kifi da ma wasu kayan da ba naci ba kamar su takin zamani da dai sauran su.

Tashar jirgin ruwan dake a Apapa dai na daya daga cikin tashoshin jirgin ruwa manya dake akwai a nahiyar Afrika inda kuma a kullum rana ake hada hadar shigowa da fita da kayyayaki zuwa kasashen duniya daban-daban.

A wani labarin kuma, Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma dan takarar neman tikitin shugaban kasar Najeriyar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP a zabe mai zuwa na 2019 watau Atiku Abubakar ya fadi ta cikin sa game da abunda zai yi idan har ya rasa tikitin takarar jam'iyyar.

Fitaccen dan siyasar yace tabbas zai taimaka da dukkan damar da Allah ya bashi don ganin jam'iyyar ta sa tayi nasara koda bai samu tikitin takarar ta ba idan dai har aka yi adalci wajen zaben.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel