Bayan komawarsa Juventus: Ronaldo zai tsallake wasanni biyu na Portugal

Bayan komawarsa Juventus: Ronaldo zai tsallake wasanni biyu na Portugal

- Dan wasan taka leda Cristiano Ronaldo ba zai bugawa kasarsa wasanni biyu dake tunkararsu ba.

- Ronaldo ya yanke wannan hukunci ne a kokarinsa na mayar da hankali kacokan ga sabuwar kungiyar kwallon kafa da ya koma

- Kwallon da ya jefa raga a garin Turin a kakar gasar cin kofin nahiyar turai, itace ta lashe kwallor da tafi kowacce

Shugaban yan wasa na kungiyar kwallon kafar Portugal Cristiano Ronaldo, ba zai bugawa kasarsa wasanni biyu dake tunkarowa ba, wadanda suka hada da wasan kasar da Italiya a gasar cin kofin kasashen turai, don bashi damar maida hankali akan sabuwar kungiyar kwallo ta Juventus da ya koma.

A cewar wani rahoto daga kafar watsa labarai ta Italiya, babban dan wasan kasar ta Portugal, na son mayar da hankalinsa kacokan ga sabuwar kungiyar kwallon kafar daya koma, tare da zama cikin garin Turin don duba lafiyar jikinsa da kuma sabawa da abokanan wasansa.

Cristiano Ronaldo, mai shekaru 33 da haihuwa, zai tsallake wasan sada zumunta tsakanin Portugal da Crotia, a ranar 6 ga watan Satumba da kuma wasansu da Italy a ranar 10 ga watan Satumba.

KARANTA WANNAN: Sabon bincike: Awaki na iya banbance mutane masu fushi da masu fara'a

Dan wasan wanda ya lashe kambun zakaran ‘yan wasa har sau Biyar, ya sanya hannu kan yarjejniyar bugawa Juventus wasa a wannan kakar wasan, daga kungiyar Real Madrid akan kudi Euro Miliyan 100.

Juventus ta samu nasarar lashe wasanni biyu a wannan gasar zakarun nahiyar turai, duk da cewa har yanzu Cristiano bai jefawa kungiyar kwallo bat un bayan komawarsa.

Dangane da zaben kwallo mafi kyawu a gasar cin kofin zakarun turai na kakar data wuce, Ronaldo ya ce: “Ina godiya ga duk wadanda suka zabi wannan kwallo da na sha. Ba zan taba manta wannan lokacin ba, musamman irin yadda masu kallo suka nuna a cikin filin da aka gudanar da wasa.”

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel