Sojojin Najeriya sun nunawa 'yan Boko Haram kwarewar aiki

Sojojin Najeriya sun nunawa 'yan Boko Haram kwarewar aiki

- Arangamar Sojoji da 'yan Boko Haram a Maiduguri ta zama ajalin uku daga cikin 'yan tada kayar bayan

- Sojijin dama ba jimawa suka yi atisayen sake kwarewa a harbi

- Kicibis dinsu da 'yan Boko Haram din ke da wuya sai suka nuna musu kwarewa a aiki

Rundunar Sojin kasar nan ta bayyana samun nasarar kashe wasu mayakan Boko Haram uku, a lokacin da suka yi musayar wuta a tsakaninsu.

Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 3 a Borno
Sojojin Najeriya sun kashe ‘yan Boko Haram 3 a Borno
Asali: Facebook

Sanarwar nasarar ta fito ne daga bakin Kakakin rundunar tsaro ta Lafiya Dole, Kanal Onyema Nwachukwu, a garin Maiduguri.

A cewarsa artabun ta afku ne kauyen Gulumba-Gana da kekaramar hukumar Dikwa.

“Jim kadan da kammala atisayen harbin bindiga da jami'anmu suka yi, mun samu nasarar kashe mayakan na Boko Haram, inda muka sami bindigogi da abubuwan fashewa".

KU KARANTA: Fusatattun matasa a Legas sun yi fito na fito da jami’an Yansanda, sun kashe Dansanda

"Muna tsaka da sintiri tare da neman maboyar ‘yan Boko Haram, sai muka yi kicibus da su, inda muka samu ababen fashewa tare da alburasai a tare da su".

Ya kara da cewa an samu alburasai da bindiga kirar AK 47 guda biyu, da kuma wata bindiga mai sarrafa kanta.

Sai dai yayin musayar wutar jami'in soji guda ya samu rauni, an kuma garzaya da shi wata cibiyar kula da lafiya, domin duba lafiyarsa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel