Idan har siyasar ka don mutane ne toh ku rungumi zaben fidda gwani – Shehu Sani

Idan har siyasar ka don mutane ne toh ku rungumi zaben fidda gwani – Shehu Sani

- Sanata Shehu Sani ya caccaki yan siyasar da suka nuna adawa da zaben fidda gwani

- Ya nuna fushin sa ne a shafinsa na twitter

- Sani ya ce hanya daa da za'a ba mutane cikakken yancinsu shie gudanar da zaben fidda gani kafin 2019

Sanata mai wakiltan yankin Kaduna ta tsakiya ya caccaki wasu yan siyasa inda ya bayyana su a matsayin matsorata masu renon tsorn mutane a zuciyarsu.

Sani ya yi wannan furucin ne ta shafinsa na Twitter @ShehuSani a ranar Alhamis, 30 ga watan Agusta.

Idan har siyasar ka don mutane ne toh ka rungumi zaben fidda gwani – Shehu Sani
Idan har siyasar ka don mutane ne toh ka rungumi zaben fidda gwani – Shehu Sani
Asali: Depositphotos

Sanatan ya ci gaba da cewa babu bukatar yan siyasa su ji tsoron idan za’ayi zaben fidda gwani tunda shine hanya guda da za’a tabatar da damokradiya sannan kuma anan ne za’a ba mutane cikakken yancin su.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, an samu gagarumin rabuwar kai a jam’iyya mai mulki ta All Progressives Party (APC) kan sabuwar tsarin gudanar da zaben fidda gwani da jam’iyyar ke shirin amfani da shi gabanin zaben 2019.

KU KARANTA KUMA: Hadimin Dogara ya shiga takarar kujerar dan majalisa na jiha a karkashin PDP

Majiya a jamiyyar sun bayyanawa jaridar Daily Trust cewa a jiya, yawancin yan jam’iyyar musamman gwamnoni sun nuna rashin yardarsu da bari mambobin jam’iyya gaba daya su kada kuri’a wajen zaben fidda gwani.

Wannan tsari ya fi kwantawa babban jigon jam’iyyar, Bola Tinubu, da shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomole.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel