An nemi Yakubu Dogara an rasa yayinda aka fara ganawar kwamitin zantarwan APC

An nemi Yakubu Dogara an rasa yayinda aka fara ganawar kwamitin zantarwan APC

- Kuma dai, Yakubu Dogara ya ki halartan ganawar jam'iyyar APC

- Ya turo wasikar neman uzuri kan rashin zuwansa

- An dade ana hasashen cewa tsoron kada a tsigeshi ya hana kakakin komawa PDP

Da alamun kaakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Yakubu Dogara, ba zai halarci taron kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC), yayinda aka fara ganawar ba tare da shi ba.

Kasancewanshi dan majalisar jam’iyyar mafi girma bayan sauya shekar shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki, yana cikin manyan masu fada aji a jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar, Kwamred Adams Ohiomole, ya karanta wasikar neman afuwan da Dogara da mataimakinsa Yusuf Lasun suka rubuto na rashin halartansu.

KU KARANTA: Buhari, Osinbajo, Tinubu sun hallara a ganawar kwamitin zantarwan APC mai muhimmanci

Kana kwatsam an ga babban jigon jam’iyyar, Asiwaju Bola Tinubu, duk da cewa bisa ga doka ba shi da hurumin halartan taron tunda bai rike da wani mukami a gwamnati.

Mun kawo muku rahoton cewa gwamnonin jam’iyyar sun yi sabani da Asiwaju Bola Tinubu ka shawarar tsarin da za’a yi amfani da shi wajen gudanar da zaben fidda gwani.

An fara ganawar misalin karfe 11:20 na safe.

An nemi Yakubu Dogara an rasa yayinda aka fara ganawar kwamitin zantarwan APC
An nemi Yakubu Dogara an rasa yayinda aka fara ganawar kwamitin zantarwan APC
Asali: UGC

Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da wasu mambobin kwamitin zantarwan jam’iyya ami mulki ta All Progressives Congress sun hallara a sakatariyan jam’iyyar ta kasa dake birnin tarayya Abuja.

Shugaba Buhari ya isa sakatariyan misalin karfe 11:19 na safen an kafin sauran masu ruwa da tsaki a jam’iyyar suka iso.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel