Hadimin Dogara ya shiga takarar kujerar dan majalisa na jiha a karkashin PDP
- Daya daga cikin hadiman kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara na neman takarar kujerar dan majalisar jiha
- Habila na neman takara ne a karkashin jam'iyyar People’s Democratic Party (PDP)
- Har yanzu Dogara bai sanar da ko ya fice daga jam'iyyar APC ba
Hasashe akan ci gaba da kasancewa kakakin majalisar dattawa Yakubu Dogara a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yawaita a ranar Laraba, 29 ga watan Agusta lokacin da daya daga cikin hadiminasa ya shiga takarar kujerar majalisar dokokin jihar Bauchi.
Iliya Habila, daya daga cikin mataimakansa a kafofin watsa labarai zai tsaya takarar kujerar dan majalisa a mazabar Bagoro karkashin jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP).
Shine zai wakilci kakakin majalisa a majalisar dokokin jihar idan har yayi nasara a zaben.

Asali: UGC
Dan majalisan, wadda bai riga yayi murabus daga matsayinsa na hadimin kakakin majalisar ba ya kasance daga mazaba daya da kakakin majalisar wakilai Dogara, wadda a yanzu ake ci gaba da kokwanto akan kasancewarsa a APC.
Tun bayan sauya shekar shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zuwa PDP idanu ya koma kan Dogara don ganin maataki na gaba da zai dauka a harkokin siyasarsa.
KU KARANTA KUMA: 2019: Matasan Arewa sun tsayar da Saraki a matsayin shugaban kasa
Har yanzu Dogara bai sanar da sauya shekarsa daga jam’iyyar APC ba, duk da cewar ya ki halartan wasu manyan tarurruka da dama da shugaban jam’iyyar ya gudanar saboda wasu dalilai.
Daya daga cikin shafukansa na zumunta a ranar Juma’a, Habila ya umurci magoya bayansa da su zo don mara masa baya a ranar Asabar a sakatariyar PDP domin sanar da jam’iyyar aniyarsa na takarar dan majalisar dokoki na jihar.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng