Zan kashe kaina idan Buhari ya fadi a zaben 2019 – Wani mutumin Abuja yayi barazana
- Wani dan Najeriya yayi barazanar kashe kansa idan har Shugaba Buhari bai lashe zaben 2019 ba
- An gano mutumin tsaye a mararraba a Abuja rike da babban kwalin sanarwar dakedauke da rubutu akan hakan
- Shugaba Buhari na neman tazarce a jam’iyyar APC
Wani mutimin Najeriya ya sha alwashin kashe kansa idan har Shugaban kasa Muhammadu Buhari bai yi nasara a zaben 2019.
Wakilin Legit.ng na yankin, Kingsley okezie ya rahoto cewa mutumin ya haifar da karamin kwaikwayo a wani gari dake Abuja lokacin da ya fito unguwanni domin yin wannan furucin.
An gano mutumin tsaye a mararraba a Abuja rike da babban kwalin sanarwa inda ya rubuta “Idan Muhammad Buhari bai ci zaben 2019 ba, zan kashe kaina”, kamar yadda yake rubuce akai.

Asali: Depositphotos
A halin da ake ciki, mun ji cewa ayyuka sun kachame a babban sakatariyar jam’iyyar Democratic Party (PDP) dake Abuja a jiya, Talata, 28 ga watan Agusta yayinda jam’iyyar ta fara siyar da fam din ra’ayi tsayawa tkara ga yan siyasar dake son takara a zaben 2019 a inuwarta.
Yayin da yan takara da dama suka biya kudin fam a asusun banki, wasu sun biya ne ta na’urar POS.
KU KARANTA KUMA: Haramci akan kodin da tramadol ya sanya ayyuka mutane 25,000 cikin hatsari – Kungiya
Daga cikin wadanda suka yanki fam din a jiya sun hada da Gwamnan jihar ombe,Ibrahim Dankwambo, wanda ke neman takarar kujerar shugabancin kasa a karkshn PDP a zaben 2019.
Bayan Dankwambo, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ma ya yaki fam din taarar shugabancin kasa a jam’iyyara jiya. Dukkansu su biyun sun biya naira miliyan biyu na nuna ra’ayi da kuma naira mliyan 10 na fam din.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng