Bidiyon yadda taron Kwankwaso ya tokare Abuja

Bidiyon yadda taron Kwankwaso ya tokare Abuja

- Duk da an hana tsohon gwamnan Kano filin kaddamar da aniyarsa ta takarar shugabancin kasar nan, ya nemarwa kansa wata mafitar

- Wani bidiyo da aka dauka lokacin taron ya nuna yadda jama'a suka yi cikar kwari don shaida yadda kaddamarwar ta kasance

Kasa da sa'o'i 24 da hana Sanata Rabiu Musa Kwankwanso yin amfani da filin taro na Eagle Square, Sanatan ya sauya gurin kaddamar da takarar shugabancin kasar nan zuwa Otel din Chida dake yankin Jabi, Abuja.

Yanzu haka dai taro yayi taro ba abinda kake gani face jajayen Huluna ta ko'ina.

Rabi'u Kwankwaso dai yayi niyyar zuwa jiharsa ta Kano a kwanan baya amma nan ma ya gamu da matsalar dakatarwa daga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje.

KU KARANTA: Wani babban basarake ya gargadi ‘yan siyasa a kan bashi toshin kudi

Yanzu dai bayan wannan kaddamar da takarar tasa ta tabbata cewa Kwankwason zai yi gwajin kwanji da manyan gwasaken cikin PDP a zaben fidda gwani na cikin gida a jam'iyyar PDP kafin daga bisani ya kara da shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ga dukkan alamu shi APC zata tsayar a zabe mai zuwa na 2019.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng