Akalla mutane 1,331 hatsarin mota ya salwantar da rayuwarsu cikin watanni Uku

Akalla mutane 1,331 hatsarin mota ya salwantar da rayuwarsu cikin watanni Uku

- Rahotanni sun bayyana cewa akalla mutane 1,331 suka rasa rayukansu a hatsarin mota, cikin watanni uku na wannan shekarar

- Rahoton da hukumar NBS ta bayar, ya nuna cewa kashi 6 na mutanen da suka mutu kananan yara ne

- A bangare daya kuma rahoton hukumar ya nuna cewa akalla mutane 8,437 suka jikkata a tsarin motoci cikin watanni uku na wannan shekarar

Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta fitar da rahoto kan adadin mutanen da suka mutu sanadin hatsarin ababen hawa, inda rahoton mai taken 'Road Transport Data (Q2 2018)' ya bayyana cewa akalla mutane 1,331 suka mutu sanadin hatsari a cikin watanni uku na wannan shekarar.

Hukumar NBS tace mutane 1,257 daga cikin 1,331 da suka mutu, wanda yake dai-dai da kashi 94 manyan mutane ne, yayin da sauran kashi 6, suka kasance kananan yara.

Kididdigar ta kuma bayyana cewa akwai maza 1,047, da suka dauki kashi 79, yayin da mata ke da kashi 21, da mutane 284, wadanda hatsarin yayi sanadin mutuwarsu.

KARANTA WANNAN: 2019: Ma'aikatan jihar Nasarawa sun tsaida Agara takarar gwamnan jihar

A cikin rahoton, hukumar ta NBS ta alakanta yawan afkuwar hadura da laifin kin bin dokokin hanya, tana mai cewa: "Rahoton watanni uku na hadurran da suka afku a Nigeria, ya nuna cewa an samu akalla afkuwar hadura 2,608. Gudu mai tsanani da kuma kin bin dokokin hanya na daga cikin dalilan faruwar haduran.

"Fashewar taya da tukin ganganci na da kashi 8.59 da kuma kashi 8.40 na silar afkuwar hadura" a cewar NBS.

NBS ta ce akalla yan Nigeria 8,437 ne suka jikkata a hadurra da dama cikin watanni uku na wannan shekarar.

Idan ba'a manta ba, Legit.ng ta ruwaito cewa hukumar kiyaye hadura da lafiyar tituna ta kasa FRSC ta fara gudanar da duba lafiyar idanun direbobi a karamar hukumar Funtua dake jihar Katsina, don magance yawan hadura da akeyi a kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel