Kato-bayan-kato: Jam'iyyar APC ya amince da sabon salon zaben fitar da gwanin ta

Kato-bayan-kato: Jam'iyyar APC ya amince da sabon salon zaben fitar da gwanin ta

- Jam'iyyar APC ta fito da sabon tsarin fitar da gwani

- Yanzu za'a yika yin kato-bayan-kato ne

- Jiya yan kwamitin gidanarwar jam'iyyar suka saukin matakin

Mambobin kwamitin koli na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a Najeriya sun amince da sabon tsarin fitar da gwani na 'yan takarar su a dukkan matakai a zaben gama gari na shekarar 2019 dake a tafe kamar dai yadda muka samu labari daga majiyar mu.

Kato-bayan-kato: Jam'iyyar APC ya amince da sabon salon zaben fitar da gwanin ta
Kato-bayan-kato: Jam'iyyar APC ya amince da sabon salon zaben fitar da gwanin ta
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: Wani Sanatan PDP na shirin komawa APC

Majiyar ta mu ta Daily Trust har ila-yau ta samu cewa wannan maganar dai ta tabbata ne a daren jiya lokacin da mambobin kwamitin da suka hada da Shugaban kasa Muhammadu Buhari, mataimakin sa da dai sauran jiga-jigan jam'iyyar suka gana.

Legit.ng ta samu cewa daman dai ba tun yanzu ba, sabon shugaban jam'iyyar na kasa Kwamared Adams Oshiomhole yayi ta nanata cewa zai tabbatar da samuwar canji a yadda ake gabatar da zabukan fitar da gwani a jam'iyyar.

Sabon tsarin fitar da gwanin dai na nufin cewa dukkan wani dan jam'iyyar yana da damar a dama da shi wajen zaben 'yan takara a jam'iyyar a maimakon wakilai kawai watau 'daliget'.

A wani labarin kuma, Wani bincike da majiyar mu ta Daily Nigerian ta gabatar, ta bankado cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da kudurin sa na yin takara a shekarar 2014 ne a ranar Laraba kuma a farfajiyar Eagle Square.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da gwamnatin tarayyar Najeriya ta hana daya daga cikin masu neman takara na jam'iyyar adawa ta PDP watau Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso filin domin kaddamar da tasa takarar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel