Har yanzu muna fama da bashin N350bn da Kwankwaso ya bari – Gwamnatin Kano

Har yanzu muna fama da bashin N350bn da Kwankwaso ya bari – Gwamnatin Kano

- Gwamnatin jihar Kano ta bayyana yadda bashi yayi mata katutu a wuya

- Ta zargi tsohon gwamnan jihar da fara ayyukan da ba zai iya kammalawa ba

Gwamnatin jihar Kano ta bakin kwamishanan yada labarai, matasa, da al’adu, Muhammad Garba, ya ce har yanzu gwamnatin jihar na biyan bashin N350bn da ta gada daga gwamnatin tsohon gwamnan jihar Rabiu Musa Kwankwaso.

Garba, wanda ya yi wannan jawabi a hira da manema labarai ya mayar da martini ne ga maganar da Kwankwaso yayi kwanan nan.

Ya ce basussukan da Kwankwaso yaci babban abin kunya ne ga gwamnatin jihar Kano.

KU KARANTA: Nan gaba kadan zamu bayyana matsayinmu kan Leah Sharibu - Fadar Shugaban kasa

“Bashin ya kunshi kwagilan gina hanyoyin sama, tituna, da kuma kudin daukan nauyin dalibai karatu a kasar waje da wasu jihohin Najeriya wanda ya kai N15bn.”

“Babu bukatan cacan baki da Kwankwaso da mabiyansa saboda kowa ya san kaidinsu.”

“Suna ikirarin cewa Kwankwaso ya gina makarantun koyar da aikin ahnnu 26, abin tambaya shine nawa daga cikin makarantun ke aiki lokacin da yake gwamna? Babu! Wasu ayyukan irin shirin Lafiya Jari da ya samar, an gaza kula da su saboda rashin gaskiya da tsoron Allan wadanda ke shugabanta wajen.”

“Titunan sama nawa Kwankwaso ya gina aka kammala kafin karewar wa’adinsa? Nawa aka gina bisa ga ka’ida a birni irin Kano? Ba’a biya yan kwangila kudadensu ba.”

“Yan kwagilan da suka bar jami’ar Maitama Sule saboda rashin kudi an biyasu yanzu. Gwamnatin Kano na kashe Miliyoyi domin bunkasa jami’ar Kimiya da Fasaha, Wudil”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel