Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu

- Amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu a bikin

- Sun nemi tallafi daga ‘yan uwa da abokansu amma sun gaza tara kudin da suke bukata

- Auren ya mutu ne sakamakon sanya babban burin yin bikin kece raini

Wata amarya da aka bayyana sunanta da Susan, ta dauki hukunci a hannunta tare da watsa wa iyayenta kasa a ido, inda ta soke aurenta da wani masoyinta, kawai don ya gaza tara dala 60,000 na yin casu a bikin.

Wannan danyen hukunci da amaryar ta dauka ya karade ko ina a kafafen sada zumunta na yanar gizo, inda jama’a ke ta cece kuce akai, tun bayan da wata ‘yar uwar amaryar ta sanya labarin a kafar Facebook da Reddit.

Labarin da ‘yar uwar amarya ta dora na cewa: “Cikin jimami nake sanar da ku cewa an soke bikin dana rigaya na sanar daku. Ina rokonku afuwa akan soke wannan biki kwanaki hudu kafin yinsa.”

Amaryar ta bayyana cewa ta yanke hukuncin soke wannan aure da saurayinta ne, bisa dalilai na kashin kanta. Bata son daga baya tazo tana zargar kawaye da ‘yan uwanta na lalata mata rayuwar aure.

Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu
Yadda amarya ta soke aurenta don mijin ya gaza tara kudin da zasuyi casu
Asali: Getty Images

KARANTA WANNAN: Naira dubu 100: Wata kabila a Arewa ta takaita kudin sadaki da bidi'o'in aure

Matar ta bayyana cewa sun hadu da saurayin ne tun suna da shekaru 14, inda suke aiki tare da gonar iyayensu.

Daga bisani suka shiga kwaleji tare, inda kowa ke sa ran kasancewarsu miji da mata, wadanda ba zasu samu wata matsala a rayuwa ba, musamman wacce shafi ta kudi.

“Mun tara akalla dala 15,000 na aurenmu. Tunda dai labarin soyayyarmu abin kwatance ne, muna son muga anyi casu a bikin, irin bikin da za’a zagaye gari ana zancensa.” A cewar matar.

“Mun zagaya wuraren da ake yin biki da dama don zabar inda zamuyi namu, amma bamu samu ba. Har sai da wani ya bamu shawarar zuwa wani wajen taro dake da tsadar gaske, amma duk wanda yayi biki a wajen, to ya kece raini.

“Da muka yi lissafi, sai muka ga muna da bukatar akalla dala 60,000 na gudanar da wannan biki, ciki kuwa harda kudin jirginmu zuwa Aruba. Don haka ne muka bukaci tallafi daga abokai da ‘yan uwanmu.”

Matar ta ci gaba da cewa: “Ta ya zamu gudanar da wannan gagarumin biki namu ba tare da kudi ba? Mun fansar da abubuwa da dama, kawai yanzu mun roki tallafin dala 1,500 daga kowane. Domin kuwa wanda duk ba zai bayar ba, to ba zamu gayyace shi ba.”

Sai dai, a nan ne labarin ya sauya, inda amarya da angon suka fahimci cewa babu wanda yake da kudirin biyan dala 1,500 don halartar wannan biki na su.

“Ganin haka yasa muka buga katin gayyata, a nan ma ba kowane ya nuna sha’awarsa ba. Gaskiya raina y abaci, me nene a cikin dala 1,000 ko 1,500 da zasu bamu tallafi? Ai a ganina wannan ba komai bane don sun bamu” a cewarta.

“Daga baya dai muka fara bin gida gida don tattara tallafin, inda muka samu dala 250 kacal. A wannan gabarce na ji na gaji, na ji na tsani auren ma gaba daya”

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel