2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau

- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar da yakin neman shugabancin kasar nan a yau

- Ana sa ran kusoshi a siyasar Nigeria dama kasashen waje zasu halarci taron

- Kwankwaso zai kara da akalla mutane 10 a zaben fitar da gwani na jam'iyar.

A yau talata ne ake sa ran tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, zai kaddamar da yakin neman tsayawa takarar shugabancin Nigeria a zaben 2019, karkashin jam'iyar PDP.

2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
Asali: Original

Asali: Facebook

A cewar wata sanarwa daga kwamitin yakin neman zabensa, Kwankwaso zai kaddamar da wannan gagarumin taro ne Chida Hotel bayan an hanasu kaddamarwa a babban filin Eagle Square dake birnin tarayya Abuja.

Jaridar Premium Times ta ruwaito mai magana da yawun Kwankwaso, Hajiya Binta Sipikin tana cewa sun samu wani sabon wurin da zasu gudanar da gangamin kaddamar da takarar Kwankwaso.

“Gangamin taron kaddamar da takarar shugaban kasa ta Sanata Rabiu Kwankwaso zai gudana ne a ranar Laraba 28 ga watan Agusta a Otal din Chida dake unguwar Utako a Abuja.” Inji ta.

2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
Asali: Facebook

Bayan kaddamar da wannan kudiri nasa na tsayawa takara, Kwankwaso zai kasance yana mai fuskantar mutane 10 a zaben fitar da gwani na jam'iyar da suma ke neman takarar shugabancin kasar.

KARANTA WANNAN: Kasar Amurka ta ce an samu karuwar cin hanci da rashawa a gwamnatin Buhari

Sanarwar ta ce tsohon ministan tsaro, kuma mamba a majalisar dattijai, zai tabbatar da gina kasar, magance matsalar tsaro da ke ciwa kasar tuwo a kwarya da kuma kare makomar kasar idan har na bashi damar zama shugabanta.

Kwamitin ya ce ana sa ran manyan masu fada aji da kusoshin siyasa daga Nigeria dama kasashen waje zasu halarci wannan taro.

2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
Asali: Facebook

Idan ba'a manta ba, Kwankwaso ya sauya sheka daga jam'iyar APC zuwa PDP da cewar jam'iyar ta gaza cika alkawuran data daukarwa al'umar Nigeria, da kuma yadda ta gaza magance rikicin shugabanci na jam'iyar, uwa uba kuma nuna wariya ga mambobinta.

2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
Asali: Original

2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
Asali: Original

2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
2019: Kwankwaso ya kwace birnin tarayya yayinda yake kaddamar da yakin zabe a yau
Asali: Original

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel